Jerin wasu labaran bogi da su ka zagaya gari a ‘yan kwanakin nan

Jerin wasu labaran bogi da su ka zagaya gari a ‘yan kwanakin nan

A ‘yan kwanakin nan, ana samun labaran karya da su ke karada gari. Wadannan labarai su kan shahara a bakuna da kafafe har a dauka cewa gaskiya ne.

Legin.ng Hausa ta tace irin wadannan labarai, ta kuma yi tankade da rairaya, ta kawo maku gaskiyar lamarin. Ga wasu daga cikin irin wadannan labarai na karya.

1. Rashin lafiyar Mamman Daura

A makon nan ne aka rika rade-radin Malam Mamman Daura bai da lafiya, bayan ganin ya tafi ganin Likita a kasar waje.

Maganar gaskiya kuwa ita ce ‘danuwa kuma aminin shugaban kasar ya na nan garau, ya je Landan ne don kawai a duba shi.

Wani na-kusa da wannan Bawan Allah, ya musanya zargin da ake yi na cewa ana tunanin Mamman Daura ya kamu da COVID-19.

KU KARANTA: Jonathan da manyan Afrika za su dura Mali gobe

Jerin wasu labaran bogi da su ka zagaya gari a ‘yan kwanakin nan
Ana zargin Evans da garkuwa da mutane
Asali: Depositphotos

2. Hukuncin kisa a kan Evans

Ana rade-radin cewa an yankewa Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans hukuncin kisa a babban kotun Legas.

Bincike ya nuna babu gaskiya a wannan rahoto, hakikanin abin da faru shi ne har yanzu ba a zartar da hukunci a kan wannan mutumi ba.

Ana zargin Evans da laifuffuka barkatai, amma kawo yanzu ba a same shi da laifi ba. Asali ma ana sauran hujjojin ‘yan sanda ne a shari’ar.

3. Bude makarantun boko

Labarin karshe a jerin rahotannin bogin na mu shi ne na bude makarantun boko. An yi ta rade-radin za a bude makarantu a watan Satumba.

Wannan rahoto na cewa ministan ilmi, Adamu Adamu ya bukaci a koma karatu gadan-gadan a cikin farkon watan gobe, ba gaskiya ba ne.

Abin da ya faru shi ne gwamnati ta yi na’am da bude makarantu ne a ranar 7 ga Satumba domin shirya jarrabawar PUTME na shiga jami’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel