Masaniyar zamantakewa ta bayyana dalilin yawaitar mutuwar aure a Najeriya

Masaniyar zamantakewa ta bayyana dalilin yawaitar mutuwar aure a Najeriya

Wata masaniyar zamantakewa a Najeriya, Ibidun Adewale, ta dora alhakin yawaitar mutuwar aure a fadin kasa a kan gazawar ma'aurata wajen shawo kan matsalarsu ba tare da saka kowa a ciki ba.

Ibidun ta ce tsoma bakin wasu daga waje da kuma rashin yarda a tsakanin ma'aurata na daga cikin manyan dalilan da ke jawo mutuwar aure.

Masaniyar, wacce ke aiki a sashen ilimi na karamar hukumar Moba a jihar Ekiti, ta bayyana hakan ne yayin tattaunawarta da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Juma'a.

Ta ce akwai bukatar ma'aurata su rungumi tsarin sulhu da tattaunawa a duk lokacin da wata matsala ta taso a tsakaninsu, a cewarta, ta hakan ne kadai za a samu zaman lafiya a gidajen aure.

"Ba kowacce matsalar aure ake dauka a kaiwa abokai, 'yan uwa, da sauran mutane da ke waje ba.

"Akwai bukatar tausayi da jin kai da bukatar kwanciyar hankali a cikin aure. Idan aka rasa hakan ne sai ma'aurata su ke tunanin wani ko wasu daga waje za su iya hada kansu, su gyara musu dangantakarsu," a cewarta.

A cewar Ibidun, yawaitar mace-macen aure na kawo matsalolin tabarbarewar zamantakewa da tattalin arzikin jama'a da al'umma baki daya.

Ta kara da cewa akwai alaka mai karfi a tsakanin yawaitar mutuwar aure da yawaitar matsalar garkuwa da mutane, fashi da makami, da sauran miyagun aiyukan laifi a Najeriya.

Masaniyar zamantakewa ta bayyana dalilin yawaitar mutuwar aure a Najeriya
Masaniyar zamantakewa ta bayyana dalilin yawaitar mutuwar aure a Najeriya
Asali: Depositphotos

Kazalika, ta shawarci ma'aurata su tuna alkawura da nauyin da suka dauka a kansu domin ta hanyar hakan ne aurensu zai dore da ransa.

DUBA WANNAN: Pantami ya shawarci matasa su rungumi wani abu guda da yafi karatun digiri muhimmanci

"Akwai bukatar a dauki wani mataki dangane da yawaitar mace-macen aure, akwai bukatar a duba lamarin.

"Mutuwar aure bata da dadi, tana haifar da abubuwa marasa dadi a tsakanin dangi da al'umma baki daya.

"Lamarin ya yi lalacewar da ma'aurata da dama sun fi yarda cewa babu wata hanya da zasu warware matsalarsu sai ta hanyar rabuwa ko saki," a cewarta.

Kwararriyar ta bawa alkalai shawarar suke bawa ma'aurata damar sulhunta kansu domin su koma su cigaba da rayuwa tare a kan ake raba aurensu.

"Yin hakan zai taimaka mtauka wajen rage yawan mutuwar aure a cikin al'umma," kamar yadda ta bayyana.

(NAN)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel