Janye gayyatar da NBA ta yiwa Elrufai: Yan Shi'a mabiya Zakzaky sun yi farin ciki

Janye gayyatar da NBA ta yiwa Elrufai: Yan Shi'a mabiya Zakzaky sun yi farin ciki

Kungiyar ‘yan uwa Musulmai ta Shi’a wacce aka fi sani da IMN ta jinjina wa matakin janye gayyatar da kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai domin ya yi jawabi a babban taronta da za a gudanar.

Kungiyar lauyoyin ta dai janye gayyatar da ta yi wa El-Rufai ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta, bayan zanga-zangar da wasu lauyoyi suka gudanar kan hakan.

A wani sako da kungiyar lauyoyin ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa ta sanar da gwamnan matakinta na janye gayyatar da ta yi masa zuwa wajen taronta.

Ta ce ta yi hakan ne sakamakon koken wasu mambobinta da ke zargin gwamnan da gazawa wajen shawo kan rikicin Kudancin Kaduna da kuma take hakkin al’umma.

Janye gayyatar da NBA ta yiwa Elrufai: Yan Shi'a mabiya Zakzaky sun yi farin ciki
Janye gayyatar da NBA ta yiwa Elrufai: Yan Shi'a mabiya Zakzaky sun yi farin ciki Hoto: PM News
Asali: UGC

Kungiyar Shi’a a cikin wata sanarwa daga kakakinta, Ibrahim Musa, a ranar Juma’a ta bayyana cewa gwamnan bai cancanci halartan taron ba, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

A gefe guda kuma, mun ji cewa El-Rufa'i ya bayyana janye gayyatar da kungiyar lauyoyin Najeriya, ta yi masa a matsayin mai jawabi a wurin taron ta da 'rungumar rashin adalci'.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun sa, Muyiwa Adeleke, ya fitar a madadinsa a ranar Alhamis, ya ce El-Rufai zai cigaba da yin tsokaci a kan batutuwan da ya ke ganin za su kawo cigaba a kasar duk da janye gayyatar.

KU KARANTA KUMA: Rundunar 'yan sanda ta sa kyautar N500K ga wanda ya tona mabuyar kwararren makashi Shodipe

"Duk da cewa NBA ce ke da ikon zabar wanda zai yi jawabi a wurin taron ta, Malam El-Rufai yana son a sani cewa dama ba shi ya nemi a gayyace shi ba kuma janyewar ba za ta rage shi da komai ba," in ji sanarwar.

"Ga ƙungiyar da ya dace ta rika bawa adalci muhimmanci, abin mamaki ne yadda ta yanke hukunci a kan al'amarin ba tare da jin ta bakin bangarorin biyu ba. Yadda suka bari matsin lamba ya canja musu ra'ayi alama ce da nuna sun rungumi rashin adalci da rashin bin doka."

Gwamnan ya ce zai mayar da martani a kan bata masa suna da aka yi a lokacin da ya sace cikin takardar ƙorafin da aka shigar a kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng