Demba Ba ya bi sahun Ozil Mesut a kan abin da ke faruwa a Yankin Uighur

Demba Ba ya bi sahun Ozil Mesut a kan abin da ke faruwa a Yankin Uighur

‘Dan wasan kasar Sanagal, Demba Ba, ya tofa albarkacin bakinsa a game da azabtar da Musulmai da ake yi a wani yanki na kasar Sin.

Demba ba wanda ya ke bugawa Istanbul Basaksehir ya na fatan sauran Taurarin ‘yan wasa za su tashi tsaye kan galabaitar da Musulman da ake yi.

Tsohon ‘dan kwallon na Chelsea da Newcastle United ya yi koyi da Takwaransa Oezil Mesut na kungiyar Arsenal wanda ya saba fitowa ya na kokawa.

A baya Oezil Mesut ya fito ya na kira da babban murya a kan zargin matsin lambar da ake yi wa ‘yanuwansa musulmai a sashen Uighur na kasar Sin.

Gwamnatin Sin ta karyata zargin da ake yi mata, amma Demba Ba ya na ganin cewa hukumomin kasar ba su yin abin da ya kamata na kare hakkin musulmai.

“Ana daukar rayukan bakaken mutane da muhimmanci ne a lokacin da wadanda ba bakaken fata ba, su ka tsaya masu.” Ba ya ke fadawa BBC.

KU KARANTA: Ramuwar gayya a rikicin Fulani da Aytab a Jihar Kaduna

Demba Ba ya bi sahun Ozil Mesut a kan abin da ke faruwa a Yankin Uighur
Demba Ba Hoto: Chelsea
Asali: Getty Images

‘Yaushe za mu ga sauran mutanen Duniya sun tsayawa Musulmai?” Demba Ba ya ke tambaya.

“Dole in shirya wani abu da ‘yan wasan kwallon kafa za su hadu, mu zauna wannan karo mu yi magana a kan batun domin da-dama ba su so a tabo lamarin.”

“Na san akwai ‘yan kwallon da su ke neman ganin an yi adalci, ko ga Musulmi, Mai addinin Buda, Kirista ko ma kowane addini.” Inji ‘dan wasan gaban.

Ba mai shekara 35 ya kara da cewa: “Ga ‘yan wasa, mu na da karfin da mu san shi ba. Idan za mu hadu, mu zauna mu yi magana, abubuwa za su canza.”

“Idan mu ka tashi tsaye, wasu za su dafa mana.”

Wannan ra’ayi ya ci karo da na Yaya Toure, wanda ya ke ganin bai dace ‘yan wasa su rika shiga siyasa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel