Buhari ya nada Amokaci a matsayin mai bashi shawara na musamman a bangaren wasanni

Buhari ya nada Amokaci a matsayin mai bashi shawara na musamman a bangaren wasanni

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsohon dan wasar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kuma jakadar kwallon kafar Najeriya, Daniel Amokaci a matsayin mai taimaka masa na musamman a kan harkokin wasanni.

Sanarwar da ofishin watsa labarai na Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Sunday Dare, ta fitar ya ce an nada shi ne a ranar 17 ga watan Agustan 2020 kamar yadda wasikar mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ta nuna.

Wani sashi na wasikar ya ce, "Ina farin cikin sanar da kai cewa, Shugaban Tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da nadin ka a matsayin mai taimakawa na musamman a kan harkokin wasanni.

"Nadin zai fara aiki daga ranar 11 ga watan Agustan shekarar 2020.”

Buhari ya nada Amokaci a matsayin mai bashi shawara na musamman a bangaren wasanni
Buhari ya nada Amokaci a matsayin mai bashi shawara na musamman a bangaren wasanni
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: Kwanel Assimi Goita ya naɗa kansa shugaban ƙasa na mulkin soja a Mali

A matsayinsa na mataimaki na musamman, ana sa ran Amokaci zai rika bawa shugaban kasa shawarwari a dukkan harkokin da suka shafi wasanni.

A farkon wannan shekarar ne aka nada tsohon dan wasan na Everton a matsayin jakadar kwallon kafa a Najeriya.

Duk da cewa mukamin ba ta da ofishi ko wasu takamamen ayyuka, ana sa ran zai rika bawa yan kwallon Najeriya da ke tasowa shawarwari.

Amokaci da ake yi wa lakabi da ‘Da Bull’, ya fara wasan kwallo ne a Kaduna a kungiyar Ranchers Bees daga nan kuma ya buga wa kungiyar Brugge ta Belgium, Besiktas na Turkiyya, Everton na Ingila da Colorado Rapids.

Ya buga wa Najeriya wasanni uku a gasar cin kofin duniya, ya ci Nations cup a matsayin dan wasa da kuma koci.

Kazalika, Amokaci ya lashe gwal a wasan kwallon Olympics na Atlanta a shekarar 1996.

Tunda rauni ya matsa masa ya dena buga wasanni, ya kasance mai horas da yan tawagar kwallon Najeriya na kasa da shekaru 23 sannan ya yi aiki a matsayin mataimakin kocin Super Eagles kuma ya yi wa Nasarrawa United koci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel