Za a fara tantance wadanda su ka nemi aikin dan sanda
A ranar Alhamis ne rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) ta sanar da cewa za a fara tantance wadanda suka nemi shiga aikin dan sanda daga ranar 24 ga watan Agusta zuwa ranar 16 ga watan Satumba, 2020.
An bukaci ma su sha'awar shiga aikin su halarci zababbun cibiyoyin tantancewa da ke fadin kasar nan sanye da fararen riguna da gajeren wando.
NPF ta bayyana cewa kowacce jiha za ta sanar da sharuda da ka'idojin da ake bukata dukkan ma su neman shiga aikin su cika.
A cewar NPF, sanarwar hakan za ta fito ne daga bakin jami'an hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda da ke hedikwatar kowacce jiha.
Sanarwar ta kara da cewa za a gudanar da tantancewar bisa da'a da biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar annobar cutar korona.
Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Frank Mba, ya bayyana cewa ana bukatar ma su neman aikin su halarci cibiyoyin tantancewa da takardun shaidar kammala karatu(orijinal da kwafi), takardar shaidar zama dan kasa, takardar haihuwa, shaidar zama dan asalin jiha/karamar hukuma, da hotuna.
Za a shirya dukkan wadannan takardu da hotuna a cikin fararen fayil guda biyu.
Kazalika, an bukaci su tafi da takardar shaidar cewa sun nemi shiga aikin dan sanda wacce su ka fitar daga yanar gizo.
DUBA WANNAN: Yadda Abacha ya kamani ya daure a 1995 bayan na ki daukan shawarar Carrington - Obasanjo
Sanarwar ta bayyana cewa ba za a saurari duk wani mai son shiga aikin dan sanda da ya gaza gabatar da cikakkun takardun da aka nema ba.
"Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya kara jaddada cewa neman aiki a rundunar 'yan sanda kyauta ne kuma za a gudanar da komai ba tare da wata rufa-rufa ba," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ya gargadi ma su neman aikin a kan su yi taka tsan-tsan da 'yan damfara da ke aika sakonni ta yanar gizo domin zambatar jama'a.
IGP Adamu ya ce za a kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifin aikata hakan, kamar yadda snarwar ta kunsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng