NBA ta janye gayyatar El-Rufa'i zuwa babban taronta na kasa

NBA ta janye gayyatar El-Rufa'i zuwa babban taronta na kasa

Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta janye gayyatar da ta yi wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, zuwa wurin babban taronta bayan wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin amincewarsu.

NBA, wacce ta saka sunan El-Rufa'i a cikin manyan baki da za su gabatar jawabi a wurin taron, ta sanar da cewa ta janye gayyatar da ta yi masa a shafinta na Tuwita a ranar Alhamis.

"Shugabannin kungiyar NBA sun gana tare da yanke shawarar janye gayyatar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, zuwa wurin babban taronta na shekarar 2020 kuma za a sanar da gwamnan wannan shawara ta hannun kwamitin tsare-tsare," a cewar sanarwar.

Kimanin mutane 3,150 ne suka rattaba hannu a kan takardar nuna rashin amincewa da gayyatar El-Rufa'i zuwa wurin taron NBA wacce wani lauya, Usani Odum, ya rubuta domin yin korafi a kan gayyatar gwamnan.

A wata takarda daban da Farfesa Koyinsola Ajayi, shugaban kwamitin tsare-tsare na taron NBA, ya fitar a kan neman a janye gayyatar El-Rufa'i, ya bayyana cewa wasu lauyoyi sun bayyana cewa sam gwamnan ba zai yi magana a wurin taron ba.

A cikin takardar wasikar mai dauke da sa hannun Silas Onu da Auta Nyada an zayyana laifuka 10 na El-Rufa'i da dansa, Bello, wanda shine mai bawa sanatan Kaduna ta tsakiya, Uba Sani, shawara.

NBA ta janye gayyatar El-Rufa'i zuwa babban taronta na kasa
Malam Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Ma su korafi sun bayyana El-Rufa'i a matsayin mai tarihin take hakkin bil'adama tare da yin korafin cewa ya gaza dakatar da kashe-kashe a kudancin jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fara dibar sabbin soji - Yadda za a nema

Lauyoyin sun yi misali da kalaman El-Rufa'i a kan zaben 2019 inda ya bayyana cewa duk wani dan kasar waje da ya shiga batun zaben Najeriya sai dai a koma da gawarsa a cikin buhu zuwa kasarsa.

Taron NBA, wanda za a yi daga ranar 24 ga Agusta zuwa ranar 26 ga watan Agusta, zai samu halartar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN)

Sauran wadanda ake sa ran za su yi magana a wurin taron sun hada da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel