Karshen magana: Dalilin da ya sa Mamman Daura ya je kasar Landan

Karshen magana: Dalilin da ya sa Mamman Daura ya je kasar Landan

Wani hadimi kuma makusancin Mamman Daura, Aminu Balele Kurfi, ya bayyana makasudin tafiyarsa Landan.

A cewar Balele Mamman Daura wanda ya kasance dan uwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tafi birnin Landan ne domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba lokaci zuwa lokaci.

Mista Kurfi na martani ne ga rahotannin ranar Laraba da ke cewa an garzaya da Mamman Daura Landan sakamakon wata rashin lafiya da ake zargin korona ce.

Da yake zantawa da jaridar Premium Times a yammacin Laraba, Kurfi ya ce: “duniya gaba daya ta ga Mamman Daura lafiyarsa kalau a ranar Talata, lokacin da ya halarci sallar jana’izar marigayi Wada Maida.”

Ya kuma ce Daura kan fita duba lafiyarsa lokaci zuwa lokaci a wajen tsoffin likitocinsa da ke zama a Ingila.

“Ina daya daga cikin wadanda suka yi masa rakiya zuwa filin jirgin sama a lokacin da ya tafi. Kuma sai da ya kirani bayan sun sauka, ya ce min sun isa lafiya. Yau dinnan Laraba ma sai da ya kira ni muka zanta.”

Karshen magana: Dalilin da ya sa Mamman Daura ya je kasar Landan
Karshen magana: Dalilin da ya sa Mamman Daura ya je kasar Landan
Asali: UGC

Ya bayyana rahotannin cewa yana cikin matsanancin rashin lafiya a matsayin ba gaskiya ba.

“A shekaru 80 a duniya yana da bukatar yawan ganin likita akai-akai,” in ji Kurfi.

Ya kara da cewa a matsayinsa na dan kasa mai yanci, Daura na da damar neman ganin likita a ko ina.

“Idan da bai da lafiya kuma rashin lafiyar ya kasance korona, kuna tunanin hukumomin Ingila za su barshi ya tafi chan ne a irin wannan lokacin?” ya tambaya.

A ranar 23 ga watan Maris Najeriya ta dakatar da sufurin jirgin sama na gida da waje a matsayin hanyar dakile korona.

Yayinda sufurin jirgin cikin gida ya dawo a ranar 8 ga watan Yuli, na waje zai dawo ne a ranar 29 ga watan Agusta.

Sai dai ba a san dalilin daga wa Mista Daura ya samu kafa ba domin ya je duba lafiyarsa.

Mista Kurfi bai fadi ba, koda dai ‘yan Najeriya da dama na ganin ya samu wannan kula ta musamman ne saboda kusancinsa da Buhari.

KU KARANTA KUMA: Rayuwa bata taba wuya irin haka ba – Audu Ogbeh ya bukaci FG ta dakatar da kashe-kashe

Ya ce masu watsa maganganun da ba daidai ba kan Mamman Daura na yi ne don saboda ya bayyana ra’ayin sa game da shugabancin Najeriya a 2023.

Kurfi ya ce Mamman Daura ya bayyana ra’ayin cewa cancanta za a bi a 2023, ba tsarin karba-karba ba.

“Menene laifi don mutum ya ce a bi cancanta a zabe ba karba-karba ba. A kudu din ma ai akwai wadanda suka cancanta sosai.

“Nan wasu suka rika ihun cewa a yi juyin juya-hali. Suka shiga zabe, jama’a suka guje su, hatta mazabarsa ko karamar hukumarsa ma bai yi nassara ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel