An kwace gawar wani jariri a wajen wata mahaukaciya bayan shafe sama da mako 1 tana yawo da shi a bayanta

An kwace gawar wani jariri a wajen wata mahaukaciya bayan shafe sama da mako 1 tana yawo da shi a bayanta

- Dakyar aka kwace wani jariri da ya shafe fiye da sati daya da mutuwa a hannun wata mahaukaciya

- An ruwaito cewa mahaukaciyar ta shafe fiye da mako daya tana yawo da jaririn a bayanta, inda har gawarshi ta fara rubewa a bayanta

- Sai da aka tara matasa masu yawa kafin a samu a yiwa mahaukaciyar wayo aka kwace jaririn aka binne a makabarta

Wata mata da aka tabbatar da cewa mahaukaciya ce ta shafe sama da mako daya tana yawo da gawar wani jariri a bayanta, mutane sun gano hakan ne bayan warin gawar jaririn ya fara damunsu.

Matar an ganta a ranar Talata, 18 ga watan Agusta, dauke da gawar yaron a karamar hukumar Effium Ohaukwu dake jihar Ebonyi.

An kwace gawar wani jariri a wajen wata mahaukaciya bayan shafe sama da mako 1 tana yawo da shi a bayanta
An kwace gawar wani jariri a wajen wata mahaukaciya bayan shafe sama da mako 1 tana yawo da shi a bayanta
Asali: Twitter

An ruwaito cewa matar ta isa wannan gari ne watanni kadan da suka wuce daga wani wuri da ba a san ko ina bane, inda ta fara zama a wani kangon gida.

Mutane basu san da zamanta a wannan waje ba har sai da mutane suka fara jin wani wari a duk lokacin da ta wuce daga gabansu, sai suka sanar da 'yan sanda bayan an bincika aka gano cewa warin na fitowa daga jikin yaron dake goye a bayanta ne.

Wata majiya ta sanar da jaridar Punch cewa: "Yan sandan sun sanar da wasu cibiyoyi guda biyu dake yankin, cibiyoyin guda biyu sun tara matasa domin kwace jaririn daga hannun mahaukaciyar.

KU KARANTA: Riham Yaqoob: Kyakkyawar budurwa da aka harbe a kasar Iraqi a yayin da take kokarin kare hakkin al'ummar kasar

"Sai dai matar taki yadda a kwace jaririn, hakan yasa aka yi ta fama da ita. Sai da matasan suka yi mata wayo sannan suka samu suka kwace gawar jaririn.

"Gawar yaron tuni har ta fara rubewa a bayanta, saboda tana goye da shi fiye da mako daya. Matasan sun kwace gawar daga wajenta inda suka binne shi a makabarta a ranar Talata."

Agbo Sunday ya tabbatarwa da jaridar Punch cewa an binne gawar jaririn a ranar Talata kuma tuni mutane sun cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba a baya.

"Mutane su koma su cigaba da kasuwancin su, saboda komai ya wuce an dauki mataki akan lamarin. An binne gawar jaririn a ranar Talata," cewar shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel