Sabon hari: Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Zangon Kataf da Maro

Sabon hari: Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Zangon Kataf da Maro

- ‘Yan bindiga sun kashe mutum goma sha daya tare da jikkata wasu da dama a sabon harin da suka kai Kaduna

- Sun kaddamar da harin ne a kauyen Ungwar Gankon da ke Zangon Kataf da kauyen Maro a karamar hukumar Kajuru

- Maharan sun kuma kona gidaje takwas inda jama’a suka tsere don guje ma wani harin na ramuwar gayya

Rahotanni sun kawo cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum goma sha daya tare da jikkata wasu da dama a sabon harin da suka kai kauyen Unguwar Gankon da ke Zangon Kataf da kauyen Maro, karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a tsakanin Litinin da Laraba.

Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan hedkwatar tsaro ta tura dakaru na musamman daga rundunar sojin sama da kasa zuwa kudancin Kaduna domin shawo kan matsalar kashe-kashe a yankin.

Koda dai hukumomin ‘yan sanda basu tabbatar da lamarin ba tukuna, Elias Manza ya fada ma Channels TV cewa harin na ramuwar gayya ne daga wasu makiyaya da suka kai farmaki garin Ungwan Gankon a daren ranar Talata sannan suka fara harbi ba kakkautawa inda suka kashe mutum biyu da jikkata wasu da dama.

Ya kuma bayyana cewa maharan sun kona gidaje takwas yayinda mazauna kauyen suka tsere daga garin saboda tsoron harin ramuwar gayya.

Sabon hari: Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Zangon Kataf da Maro
Sabon hari: Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Zangon Kataf da Maro Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shugaban ya kuma bayyana cewa dakaru na musamman na sojin kasa da sama sun isa wasu daga cikin garuruwan a kokarin kare mazauna yankin daga harin ‘yan bindiga.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe sojoji 3 da 'dan sa kai 1 a Niger

Shugaban karamar hukumar Kajuru, Cafra Caino, ya kuma tabbatar da cewar ‘yan bindiga sun kashe mutum hudu da ke tafiya a motar kasuwa a kauyen Maro, wani iyaka tsakanin kananan hukumomin Kajuru da Kachia.

Ya yi bayanin cewa ‘yan bindigan sun kama motar kasuwar daga jeji da rana, sai suka harbe mutum hudu da ke ciki harda wani fasto, sannan Daga bisani suka tafi da direban zuwa wani waje da ba a sani ba.

‘Yan bindigar sun aiwatar da hare-hare makamancin wannan a kauyen Bugai kusa da Banikanwa a karamar hukumar Kachia a daren ranar Litinin, sannan suka kashe mutum biyar ciki harda hakimin kauyen da mahaifiyarsa, yayinda wasu da dama suka jikkata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel