Rashin hankaline ace daliban da suka gama jami'a da sakamako mai kyau suna neman aiki - Muhammad Akanbi
Babu alamun hankali ace dalibi zai kammala jami'a da sakamako mafi rinjaye sannan kuma ya fita ya fara neman aiki, cewar shugaban jami'ar jihar Kwara Muhammed Akanbi
Mataimakin shugaban jami'ar jihar Kwara, Muhammed Akanbi, ya ce babu alamun hankali ace daliban da suka gama jami'a da sakamako mafi rinjaye suna neman aiki a Najeriya.
Akanbi yana martani akan kididdigar da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar na cewa akwai 'yan Najeriya miliyan 21.76 da basu da aikin yi.
A yadda rahoton ya fitar yawan marasa aikin yin a Najeriya ya karu daga miliyan 20.93 a shekarar 2018 zuwa miliyan 21.76 a shekarar 2020.
Da yake magana a lokacin da ya jagoranci hukumar makarantar zuwa wasu daga cikin manyan ma'aikatu na kasa dake Abuja domin neman taimako ga jami'ar, Akanbi ya ce bai kamata ba ace jami'a ta yaye dalibai da sakamako mafi rinjaye ba tare da wata kwarewa ba wajen sana'o'i.
Ya ce babban abinda jami'ar shi ta sanya a gaba shine koyar da sana'o'i da kuma kawo cigaban al'umma, ya kara da cewa jami'ar tana so ta dinga yaye dalibai da kwarewar da zasu iya samawa wasu aikin yi.
KU KARANTA: An kwace gawar wani jariri a wajen wata mahaukaciya bayan shafe sama da mako 1 tana yawo da shi a bayanta
"Tuni muna bawa daliban mu karfin guiwar koyon sana'o'i, sannan kuma su dauki takardu da muhimmanci. Babu alamun hankali ace ka gama da sakamako mafi rinjaye kuma ka fita kana neman aikin yi. Kuma ina nufin sakamako mafi rinjaye a kowanne fanni na karatu," ya ce.
"Jami'ar mu jami'a ce ta kawo cigaban al'umma da kuma koyar da sana'o'i. Muna da cibiya wacce muka gyara, wacce yanzu ake kiranta da cibiyar koyon sana'o'i da kere-kere, saboda bama so mu koyar da sana'o'i kawai a takarda.
"Muna sanya daliban mu a harkoki na koyon kere-kere. Zaku ga dalibi ya bada himma wajen koyon yadda ake kera takunkumi na fuska, abin wanke hannu, wasu suna koyon dinki, wasu kafintoci, wasu kuma na koyon yadda ake gyaran mota da sauran su."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng