Mai bada shawara na musamman a fannin lafiya ga gwamnan Kwara ya yi murabus

Mai bada shawara na musamman a fannin lafiya ga gwamnan Kwara ya yi murabus

- Mai bada shawara na musamman a fanni lafiya ga gwamnan jihar Kwara, Farfesa Wale Sulaiman ya yi murabus

- Farfesan ya bayyana cewa, burin da yake da shi na bincike da fadada ilimi a fannin lafiya a duniya ne yasa ya ajiye aikin

- Gwamna Abdulrazak ya nuna godiyarsa a kan gudumawar da Farfesan ya bai wa gwamnatinsa tare da yi masa fatan alheri

Mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar Kwara, Mallam Abdulrahman AbdulRazaq, a fannin kiwon lafiya, Farfesa Wale Suleiman, ya yi murabus.

Gwamnan ya sanar da cewa Birgediya Janar Saliu Tunde Bello, shine zai maye gurbinsa.

Ya kara da sanar da cewa, Aliyu Muyideen ne sabon mataimaki na musamman ga gwamnan a fannin yada labarai.

Wannan na kunshe a wata takardar da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Rafiu Ajakaye, ya fitar a daren Laraba.

Kamar yadda takardar ta bayyana, gwamnan ya nada Adekunle David Dunmade, a matsayin sabon mai bada shawara garesa na musamman a fannin lafiya.

Dunmade dan asalin Ifelodun, ya maye gurbin Wale Sulaiman, wanda ya ce ya bar matsayinsa ne don fadada aikinsa a fannin lafiya na duniya.

A takardar murabus dinsa, ya ce: "Sakamakon ra'ayi mai karfi da Farfesa Wale Sulaiman ke da shi a fannin lafiya na duniya, kofofinmu a bude suke garesa da sauran masu fatan ganin ci gaban jihar Kwara. Muna alfahari da ku.

Mai bada shawara na musamman a fannin lafiya ga gwamnan Kwara ya yi murabus
Mai bada shawara na musamman a fannin lafiya ga gwamnan Kwara ya yi murabus. Hoto daga Within Nigeria
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan yarinyar da fasto ya sace na tsawon shekaru 7, ta dawo gida

"Gwamnatin za ta ci gaba da tuntubar Farfesa Wale Sulaiman a kan duk abinda ya shige mata duhu na fannin lafiya.

"Gwamnan yana jinjinawa gudumawar da Farfesa Wale Suleiman ya bada a kan aikin da yayi tare da shi da kuma nasarorin da aka samu a habakar fannin kiwon lafiya. Hakan ya hada da yaki da annobar korona.

"Gwamnan yana mika godiyarsa ta musamman tare da fatan alheri garesa a duk inda zai saka kafa."

Sabon mai bada shawara na musamman ga gwamnan Kwara a fannin tsaron, Birgediya Janar Bello, wanda ya fito daga yankin Erin Ile a karamar hukumar Oyun, tsohon gwamnan jihar Kebbi ne na soja tsakanin 1993 zuwa 1996.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: