Kungiyar SOKAPU ta ce an kashe mutane 11, mutum 5 sun mutu a Zongon-Kataf

Kungiyar SOKAPU ta ce an kashe mutane 11, mutum 5 sun mutu a Zongon-Kataf

Kungiyar SOKAPU ta mutanen kudancin jihar Kaduna, ta na ikirarin an kashe mata mutum 11, daga ciki har da wani Mai unguwa da mahaifiyarsa mai shekaru 97.

A cewar wannan kungiya mai kare al’ummar yankin jihar Kaduna, wasu ‘yan bindiga ne su ka yi wannan danyen aiki a kananan hukumomin Zango-Kataf, Kajuru da Kachia.

Wannan jawabi ya fito ne ta bakin sakataren yada labarai na SOKAPU, Luka Binniyat. Ya ce a yanzu garuruwa 109 da ke yankin kudancin Kaduna su na hannun ‘yan bindiga.

Mista Luka Binniyat ya ce an shiga kauyen Unguwan Gankon a Zangon Kataf, an kashe mutane biyu; Kefas Malachy Bobai da wata ‘yar makaranta mai suna Takama Paul.

Sauran wadanda ake zargin ‘yan bindigan sun kashe sun hada da Fasto Adalchi Usman wanda ya ke limanci a wani coci da ke Unguwan Madaki a karamar hukumar Kajuru.

Duk a wannan lokaci a makon da ya gabata, an hallaka Mariah Na’Allah, Mista Shekari, da Ezekiel Maikasa. Wadannan mutane sun fito ne daga Zangon Kataf da Kajuru.

KU KARANTA: Ana zargin wani Mai ba Gwamna shawara da bada umarnin kashe ‘Yan adawa

Kungiyar SOKAPU ta ce an kashe mutane 11, mutum 5 sun mutu a Zongon-Kataf
Sufeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya Hoto: NPF
Source: Facebook

Har ila yau a ranar Lahadin da ta wuce, an kai hari a kauyen Bugai da ke cikin garin Kachia.

A Bugai, an yi rashin dace an kashe Mai unguwar Dan’azumi Musa An kuma kashe ‘yanuwansa, Aniya Musa da Angelina Irmiyam da uwarsu Kande Musa mai shekara 87.

Luka Binniyat ya ce duk da an sa dokar hana fita, ana cigaba da kashe-kashe. Ya ce akwai mutane fiye da 50, 000 da ke fake a sansanin gudun hijira, sakamakon raba su da aka yi da gida.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa rigimar Atyab da mutanen Fulani a kudancin jihar Kaduna ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar a wasu danyun hari a makon nan.

An kashe mutane akalla biyu, sannan an kona gidaje bakwai a Unguwan Gankon, a dalilin kashe wasu Fulani uku a garuruwan Tukabe, Ikulu da ke karamar hukumar Zangon Kataf.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel