Mun gaji da gafara sa: Daliban jami'a sun fara zanga-zanga a Najeriya kan rufe makarantu
Wani rahoto da muke samu ya nuna cewa daliban jami'a sun fara gabatar da zanga-zangar lumana a jihar Kwara, inda suka bukaci gwamnati ta bude makarantu kamar yadda ta bude sauran wurare a fadin kasar
A jiya Laraba ne 19 ga watan Agusta daliban jami'a a jihar Kwara suka fara gabatar da zanga-zanga, inda suka bukaci gwamnati ta bude makarantu jami'a a jihar.
Tun cikin watan Maris ne dai gwamnatin tarayya ta rufe makarantun jami'o'i a fadin Najeriya a kokarin da take na dakile yaduwar annobar coronavirus a fadin kasar.
Kamar yadda jaridar Linda Ikeji ta wallafa a shafinta daliban masu gabatar da zanga-zangar sunyi tattaki har zuwa bakin gidan gwamnatin jihar dake garin Ilorin babban birnin jihar. Sun ce idan har za a bude filin tashi da sauka na jiragen sama, sannan a bude kasuwanni, da Masallatai da coci, mai yasa za a cigaba da rufe makarantu?
Sun dauki alluna dauke da rubutu a jiki da suke nuni da bukatarsu ga gwamnati, inda a jikin wasu allunan aka yi rubutu kamar haka: "Adamu ka ceto karatunmu", "A bude makarantun jami'a yanzu".
KU KARANTA: Zamu sanya ido akan hukuncin kisa da aka yankewa wanda ya zagi Annabi a Kano - Kasar Birtaniya
Ga dai wasu daga cikin hotunan zanga-zangar da daliban suka gabatar a kasa:
Yayin da ake wannan tataburzar a Najeriya, wani rahoto da Legit ta samo daga jaridar Daily Trust ya nuna cewa jami'ar Oxford ta kasar Ingila ta nuna ra'ayinta wajen aiki da tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi.
Kamar yadda cibiyar ta ce, Sanusi, wanda aka tube wa rawani a farkon shekarar nan, ya yi niyyar amfani da wannan lokacin don rubuta littafi a kan yadda za a yi martani ga matsalar kudi a duniya.
Cibiyar ta sanar da cewa zai yi amfani da gogewarsa a matsayin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, kuma a matsayin ma'aikacin bankin da gogaggen wanda ya saba mu'amala da jama'a.
A yayin zantawa da Daily Trust a daren jiya, daraktan cibiyar, Farfesa Wale Adabamwi, wanda dan Najeriya ne, ya ce:
"Ina matukar farin ciki da zai zo cikinmu a watan Oktoban. Zai zama babban ci gaba ga abinda muke yi. Zai yi aiki a kan bincikensa kuma zai dinga amfani da gogewarsa don dalibai da manazarta."
Sanusi, masanin tsumi da tattali kuma ma'aikacin bankin, ya yi aiki a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya daga 2009 zuwa 2014.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng