EFCC: Musamman aka nemi in tona asirin Magu – Giwa ya fadawa kwamitin Salami
Victor Giwa, wani Lauya da ke Abuja, ya ce an dauko shi haya ne da nufin a cafke tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC watau Ibrahim Magu.
Kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa karkashin Ayo Salami ya na binciken ayyukan da EFCC ta yi a lokacin da Ibrahim Magu ya ke rike da hukumar.
Ana zargin Magu da karkatar da kudin da hukumar EFCC ta karbo daga hannun barayin gwamnati, da kuma saida kadarorin da aka karbe ga abokai da na kusa da shi.
A wata takarda da Donald Wokoma ya rubutawa kwamitin shugaban kasa da ke binciken Magu, ya zargi tsohon shugaban EFCC da neman cin hancin Naira miliyan 75.
Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto a ranar Talata, Wokoma ya ce Ibrahim Magu ya bukaci a ba shi cin hanci ne ta hannun tsohon lauyansa, Victor Giwa.
Mista Wokoma ya gabatar da faifen sautin murya a gaban kwamitin Ayo Salami inda aka ji tattaunawarsa da Victor Giwa, a matsayin hujja a kan Ibrahim Magu.
KU KARANTA: Magu ya yi raddi, ya zargi Minista da kawo cikas a binciken Diezani
A wata takarda da aka fitar a ranar 15 ga watan Agusta, Giwa ya maida martani, ya ce Wokoma ya nemi ya yi amfani da shi ne domin ayi ram da tsohon shugaban na EFCC.
Ya ce: “Ni Victor Giwa, na bukaci na bada karin bayani, ina shaida cewa takardar korafin da aka fitar ta fito ne sakamakon matsa mani da Donald Wokoms ya yi saboda ayi ram da tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu.”
Victor Giwa ya kara da cewa: “An yi haka ne da alkawarin za a fito masa da kudinsa”
Lauyan ya ce bai bada hadin kai wajen wannan shiri ba. “Gardamar da na yi ne ya jawo aka gabatar da faifen sautin tattaunawata da wani, wanda bayani ne na sirri.”
Takardar lauyar da ta shiga hannun kwamitin ta kare da cewa: “Zan yi godiya idan har aka ba ni damar bada karin hujjoji.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng