An yanke hukuncin kisa ga barawon doyar da ya kashe mai gona

An yanke hukuncin kisa ga barawon doyar da ya kashe mai gona

- Babbar kotun Ado Ekiti, ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kisan kai da yayi

- Matashin mai suna Dele Ojo ya je sata ne a gonar doya sannan ya kashe mai gonar bayan kama shi da yayi yana masa barna

- Mai shari’a Abiodun Adesodun ya bayyana cewa ya zartar da hukuncin ne sakamakon hujojjin da aka gabatar a gaban kotun wanda suka tabbatar da cewar Dele ya aikata laifin

Wata babbar kotun Ado Ekiti, jihar Ekiti ta yanke wa wani matashi mai shekaru 26 wanda aka ambata da suna Dele Ojo hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kisan kai da yayi.

Mai shari’a Abiodun Adesodun ya bayyana cewa ya zartar da hukuncin ne sakamakon hujojjin da aka gabatar a gaban kotun wanda suka tabbatar da cewar Dele ya aikata laifin da ake tuhumarsa a kai a ranar 13 ga watan Satumban 2018.

Mai gonar doyan da mai laifin ya je sata a gonarsa ya dade yana fakon barawon da ke girbe masa doya domin kusan kullum idan ya garzaya gonar sai ya iske an yi masa barna.

A ranar da asirin Dele ya tonu sai aka kamashi yana hakar doyan yana dankara wa a wani katon buhu.

An yanke hukuncin kisa ga barawon doyar da ya kashe mai gona
An yanke hukuncin kisa ga barawon doyar da ya kashe mai gona Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Daga nan sai mai gona, Adebowale da yake ya gane mai laifin ne ya ke masa sata, sai ya kwala masa kirar sunansa, juyawansa ke da wuya sai ya dirka masa wata bindigan da yake rike da ita ya tsere abinsa.

Adewole ya rasu a asibitin Ijero dake Ekiti bayan garzayawa da aka yi dashi chan cikin gaggawa.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe sojoji 3 da 'dan sa kai 1 a Niger

Lauyan da ya shigar da Karar, Wale Fapohunda wanda kuma shine atoni-janar na jihar, yayin shari’an ya kira shaidu hudu, ciki harda jami’in dan sandan da ke binciken lamarin da kuma wani likita.

Sauran kayayyakin da aka gabatar sun hada da bindigar toka, hotunan marigayin, doya guda biyar, jawabin wanda ake zargi a lokacin da yake amsa laifinsa da sauran takardu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel