Babbar magana: An garkame mai kamfanin gidajen mai na Rahamaniyya a kasar Burtaniya

Babbar magana: An garkame mai kamfanin gidajen mai na Rahamaniyya a kasar Burtaniya

An yanke wa wani shahararren dan kasuwar man fetur kuma shugaban gidan man Rahamaniyya Oil and Gas Limited, Abdulrahman Bashir hukuncin watanni 10 a gidan yari a kasar Ingila.

A watan Fabrairu, Justis Butcher na babbar kotun Ingila da Wales ya yanke cewa a tsare Bashir a gidan kurkuku saboda kotu ta same shi da laifin raina kotu da karya umarninta ba sau daya ba, a wata kara da kamfanin mai na Sahara Energy Resources Ltd su ka shigar.

“Dalilin hukuncin ya kasance cewa Mista Bashir ya yi ta saba umurnin Mista Justis Robin Knowles na ranar 1 ga watan Agusta 2019 da kuma umurnin Mista Justis Bryan na ranar 6 ga watan Satumba 2019,” cewar hukuncin.

Kotu ta bada umarnin cewa mai Rahamaniyya Oil and Gas ya bai wa kamfanin Sahara Energy Resources Ltd metrik tan 6,400.69 na man gas.

Kotu ta nemi Abdulrahman Bashir ya sa kamfanin sa Rahamaniyya Oil and Gas ya bada wannan lodin dimbin mai a tashar lodin jirage masu jigilar mai ta bakin ruwan Kirikiri, Apapa da ke Lagos.

Babbar magana: An garkame mai kamfanin gidajen mai na Rahamaniyya a kasar Burtaniya
Babbar magana: An garkame mai kamfanin gidajen mai na Rahamaniyya a kasar Burtaniya Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Bashir ya karya wannan umarni ta hanyar kasa bai wa kamfanin sa Rahamaniyya Oil and Gas umarnin bada man gas din ga Sahara Energy, a tashar jiragen ruwa ta Apapa.

Kotun ta kuma bayar da bayanin cewa ana iya sassauta hukuncin zuwa watanni shida idan Mista Bashir ya bayar da hadin kai ga umurnin da ya take a baya.

An ci tarar Rahamaniyya £ 500,000 yayinda aka ci tarar manajan, Adebowale Aderemi tarar 10,000, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Lamarin dai ya faro ne cikin watan Yulin 2019, Ultimate Oil and Gas, wanda reshe ne na Rahamaniyya, ya kulla yarjejeniya a rubuce shi da Sahara Energy.

A cikin yarjejeniyar an gindaya cewa kamfanin Rahamaniya zai rika adana man gas a rumbun ajiyar ta da ke tashar jiragen ruwa ta Lagos, har sai bayan Ultimate ya gama biyan kudaden.

Bayanan kotu sun nuna cewa a bisa yarjejeniyar da aka kulla, Sahara Energy ya tura metrik tan na man gas har 14, 967, 159 ga Rahamaniyya a tashar jiragen ruwa, a Lagos.

Sahara Energy ya aika da rasidin shaidar ya aika da man gas a ranar 26 Ga Disamba, 2019, kuma ya nemi a biya shi kudin sa har dala miliyan 10,760,768 77.

A ranar 29 ga watan Agusta, 2019 ne ya kamata a ce an biya kudaden gaba daya.

Takardun kotu sun nuna yadda aka rika kai-ruwa-rana wajen biyan kudade.

An gano cewa tun ma daga nan Najeriya ne aka fara shigar da karar laifin karya ka’idojin da ke shimfide a cikin jarjejeniyar da suka kulla.

Yayin da aka ci gaba da shari’a a Babbar Kotun Ingila, sai Bashir mai Rahamaniyya ya ki bin umarnin kotu ba sau daya ba, ciki har da hukuncin da ya daure shi a kurkuku.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Gwamnan Nasarawa ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa

Maimakon Rahamaniyya ya bi doka, sai ya nemi kotu ta janye hukuncin da ta yanke a kan ta a bisa abin da ya kira uzirin rashin lafiya da rashin isar da sako kan lokaci.

Daga nan mai Rahamaniyya ya yi alkawarin biyan kudin. Daga baya kuma ya sake yin watsi da batun kudaden.

An yi ta tsugune-tashi da lauyan Rahamaniyya a kotu, shi kuma ya ki gabatar da kan sa, ballantana ya biya kudaden.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel