Alkaluman NBS sun nuna kaya sun kara tsada da kashi 12.2% a watan Yuli
Sababin alkaluman da aka fitar na hauhawar kudin kaya wanda ake aunawa da farashi a kasuwanni, ya nuna kaya sun tashi da kashi 12.82% a Yuli.
Rahotanni sun ce wannan tashi da kaya su ka yi da kusan kashi 13% a watan jiya shi ne mafi yawan tsadar da aka gani a kasuwanni cikin watanni 27 da su ka wuce.
Hukumar tara alkaluma na kasa watau NBS a rahoton da ta fitar a ranar Litinin, 17 ga watan Agusta, 2020, ta ce an samu kari daga farashin watan Yuni.
A watan Yuni, an tsaida tashin farashin kaya a kan 12.56%, hakan ya na nufin an samu karin tsadar kaya a kasuwanni da 0.26% a watan da ya gabata.
Tun da aka shigo wannan shekara ta 2020, kaya su na ta kara tashi ne a kasuwa. Babu watan da aka samu sauki a farashi daga Junairu har zuwa yanzu.
Ga yadda alkaluman farashi su ke daga Junairu, Fubrairu, Maris, Afrilu, Mayu da Yuni: 12.13%, 12.20%, 12.26%, 12.34%, 12.40% sai 12.56%.
KU KARANTA: Duk bayan kwana biyu sai an sace mutane 7 a Najeriya

Asali: Twitter
A lissafin wata-wata, za a ga cewa farashin kaya a Najeriya sun tashi da 1.25% a Yuli. Hauhawan farashin ya yi sama da 0.04% na abin da aka samu a baya.
Hukumar NBS ta ce a birane an tsaida tashin farashi a a kan 12.5%, a kauyuka kuma alkaluma sun nuna an samu hauhawan farashi na 11.49%.
Cikin fiye da shekaru biyu da su ka gabata, farashin kaya ba su yi irin wannan tashi ba. Hakan ya nuna yadda abinci da kayan masarufi su ke kara tsada a kasar.
An samu wannan hauhawan farashi ne a sakamakon tsadar da burodi, hatsi, dankali, doya da sauran kayan abinci irinsu nama, mai, da kifi su ka yi.
Kayan gona sun kara tsada da 10.10% a watan jiya, akasin abin da aka samu na hauhawan farashi na 10.13% a watan Yuni inji hukumar.
Rahoton da aka fitar ya nuna an fi samun wannan tashin farashin kaya a Kogi, Sokoto, Bauchi da Filato. Abin bai yi kamari sosai a Legas, Adamawa, da jihar Kwara ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng