Kisan kai: 'Yan sanda sun damke basarake, 'ya'yansa 2 da kungiyarsa ta daba

Kisan kai: 'Yan sanda sun damke basarake, 'ya'yansa 2 da kungiyarsa ta daba

Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Legas sun damke wani mutum da ke ikirarin zama basarake mai shekaru 72 mai suna Lateef Olarinde, dan shi da wasu mutum uku a kan zarginsu da ake da kashe-kashe tare da wasu ayyukan tada tarzoma a birnin Oguntedo da ke jihar.

Sauran mutum hudun sun hada da Yusuf Olarinde mai shekaru 38, Kazeem Sadiku mai shekaru 35, Sanni Olarinde mai shekaru 37, Ayomide da Babatunde Lateef.

Kamensu ya biyo bayan korafe-korafen mazauna yankin a kan miyagun ayyukan Olarinde da sauran 'yan kungiyarsa da kuma umarnin da 'yan sandan suka samu daga kwamishinan 'yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, na su damko wadanda ake zargi.

Jami'an 'yan sandan sun ce Olarinde ya kasance cikin wadanda ake nema ido rufe a yankin, sakamakon kisan kai da tada tarzoma.

An gano cewa, daya daga cikin 'ya'yansa ya shiga hannun 'yan sanda kusan wata daya da ya gabata, kuma bayanansa ne suka sa aka kama mahaifinsa a ranar 21 ga watan Yulin 2020.

Kisan kai: 'Yan sanda sun damke basarake, 'ya'yansa 2 da kungiyarsa ta daba
Kisan kai: 'Yan sanda sun damke basarake, 'ya'yansa 2 da kungiyarsa ta daba. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ka fada wa jama'a malaman da ke son kudi ko ka rufe mana baki - Fasto ya caccaki El-Rufai

A yayin damko wadanda ake zargin a gaban manema labarai, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya kwatanta Olarinde da shugaban "gagarumar kungiyar 'yan ta'addan da ta addabi yanki da kewaye."

Odumosu ya ce, an samu gawar wani mutum daya da ake zargin Olarinde da yaransa ne suka kashe kuma suka kona shi don batar da kamanninsa.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce, "babban wanda ake zargin, ya yi ikirarin zama mai sarauta a yankin Oguntedo. Ya saba tara matasa da makamai inda suke tada tarzoma a yankin Ashaogun na tsawon lokaci.

"Harin su na zuwa ne da harbe-harbe tare da kashe rayukan wadanda basu san komai a kai ba. Bayan harin, wadanda ake zargin su kan koma maboyarsu."

Odumosu ya zargi cewa, a ranar 18 ga watan Maris na 2020 da kuma 18 ga watan Yulin 2020, kungiyar 'yan daban ta kashe wani mutum daya inda ta raunata wasu masu tarin yawa.

"An samu harsasai masu rai daga wurin wadanda ake zargin," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel