Edo: Oshiomhole da Gambari ba su da niyyar sa a cafke ‘Yan PDP – Garba Shehu

Edo: Oshiomhole da Gambari ba su da niyyar sa a cafke ‘Yan PDP – Garba Shehu

Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana zargin da ake yi na cewa wasu manya a gwamnati su na da niyyar kama ‘yan adawa a zaben Edo, da matsayin karya da yaudara.

Wani gajeren bidiyo ya na yawo wanda ‘yan hamayya su ke amfani da shi a matsayin hujjar shirin yi wa manyan PDP dauki dai-daya a zaben gwamnan jihar Edo da za ayi kwanan nan.

An fara yama-didi da wannan faifen bidiyo ne a jiya, jim kadan bayan tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya ziyarci fadar shugaba Muhammadu Buhari.

Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya fitar da jawabi a ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2020, ya na mai cewa bidiyon shirin wasu bata-gari ne.

“Ya na da muhimmanci mu karyata sakonnin da ake yawo da shi tsakanin ‘yan jarida, masu tofa albarkacin bakinsu, ‘yan gwagwarmaya da waya da kan jama’a game da wani gajeren faifen bidiyo da ake ikirarin shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, sun kitsa yadda za a damke ‘yan adawa gabanin zaben jihar Edo.” Inji Garba Shehu

Malam Garba Shehu ya kara da cewa: “Na farko, ya na da muhimmanci ace wannan bidiyo, danyen aikin wasu miyagu ne da aka zakulo daga cikin maganar kirki da ake yi game da hatsaniyar da ta ke tasowa daf da zaben nan.”

KU KARANTA: ‘Yan Sanda sun cafke mutane 15 da su ka kai hari kan Tawagar Gwamna

Edo: Oshiomhole da Gambari ba su da niyyar sa a cafke ‘Yan PDP – Garba Shehu
Garba Shehu ya wanke Oshiomhole
Asali: UGC

“Sanannen abu ne cewa jam’iyyun siyasa da su ka shiga takara a Edo su na zargin junansu da tada rigima.”

“A irin wannan yanayi na rashin tabbas, shugabannin da su ka san abin da su ke yi, za su tabbatar cewa an yi zabe cikin zaman lafiya, an yi aiki da jami’an tsaro wajen kare ran jama’a.”

Shehu ya ce wannan zai taimaka wajen hana ‘yan iskan gari kawo matsala a harkar zabe.

“Shugaban kasa ya saba fadan wannan magana da babbar murya.” Ya kuma ce: “Ba ya goyon bayan rigima ko na sisin-kobo. Za a kama wadanda su ka tada ta.”

A dalilin wannan Shehu ya ce Gambari da Oshiomhole ba za su taba jefa kansu cikin harkar da zai jawo fitina ko a murde zaben gwamnan da za ayi a jihar Edo ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng