Kungiyar Barcelona ta sanar da daukan Koeman a matsayin sabon kociya

Kungiyar Barcelona ta sanar da daukan Koeman a matsayin sabon kociya

Da yammacin ranar Talata ne kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke kasar Andolus (Spain) ta sanar da daukan tsohon dan wasanta na tsakiya, Ronald Koeman, a matsayin sabon mai horar da 'yan wasanta.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Josep Maria Bartomeu, ne ya sanar da hakan a jawabin da ya gabatar ranar Talata.

"Koeman zai kasance sabon kociyan kungiyar Barca daga zangon wasa na gaba," a cewar Bartomeu a sanarwarsa da aka nuna a gidan talabijin na kungiyar Barcelona.

Koeman, kociyan kungiyar kwallon kafa ta kasar Netherlands tun shekarar 2018, zai maye gurbin Quieque Setien, tsohon kociyan da aka kora bayan kungiyar Bayern Munich ta kasar Jamus ta lallasa Barcelona da ci 8 - 2 a gasar zakarun Turai.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da fatattakar Setien a ranar Litinin, 17 ga watan Agusta.

Kungiyar Barcelona ta sanar da daukan Koeman a matsayin sabon kociya
Ronald Koeman
Asali: Getty Images

Barcelona ta sanar da sallamar kocin nata a wata takarda da ta fitar a shafinta na yanar gizo, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Ta ce: "Majalisar daraktoci ta amince da sallamar Quique Setien. Don haka daga yanzu ya tashi daga kocinta.

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamnatin tarayya ta magantu kan ranar bude jami'o'i

"Wannan ne hukunci na farko da aka fara dauka yayin da ake fara kawo sabbin gyare-gyare a kungiyar wanda daraktocin suka aminta da su. Za a sanar da sabon kocin nan da kwanaki kadan."

Setien ya samu matsuguni a kungiyar kwallon kafar ta Barca a ranar 13 ga watan Janairu bayan fatattakar kocinta Ernesto Valverde da ta yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel