NDDC: Na yi mamaki da na ji wasu su na tunanin suman karya na yi – Farfesa Pondei

NDDC: Na yi mamaki da na ji wasu su na tunanin suman karya na yi – Farfesa Pondei

Mukaddashin shugaban ma’aikatar NDDC mai kula da cigaban Neja-Delta, Kemebradikumo Pondei, ya yi magana game da abin da ya faru da shi kwanaki.

Kwanakin baya Farfesa Kemebradikumo Pondei ya sume a yayin da ya ke amsa tambayoyi a gaban ‘yan majalisa, wasu su na ganin akwai alamun tambaya game da sumar.

Kemebradikumo Pondei ya yi magana da jaridar Vanguard a ranar Talata, ya ce wani irin mummunan ciwo ne ya auko masa lokacin da ya ke gaban ‘yan majalisa.

“Na samu wani irin ciwo ne da ban san kan shi ba da ya mamaye ni. Abin mamaki ne wasu su rika tunanin sumar karya na ke yi.” Inji Farfesa Kemebradikumo Pondei

Pondei ya kara da cewa: “Ba na fatan wani ya ji irin abin da na ji a wancan lokaci. Ni ba na tserewa bincike. Na yi watsi da duk wannan lamari da ya faru yanzu.”

A game da jinkirin da aka samu game da amincewa da kasafin kudin NDDC a majalisa, ya ce: “Tuntuben alkalami aka samu, sai mu ka bukaci karin minti goma, mu yi gyara.”

KU KARANTA: Dole mu binciki aron da Gwamnati Tarayya ta ke yi - Majalisar Wakilai

NDDC: Na yi mamaki da na ji wasu su na tunanin suman karya na yi – Farfesa Pondei
Farfesa Kemebradikumo Pondei
Asali: UGC

Pondei ya karyata zargin da ake yi na cewa kwamitin rikon kwaryar da ya ke jagoranta sun yi sama da fadi da kudi. Ya ce babu gaskiya a zargin da majalisa ta ke yi wa EIMC.

Farfesan ya ce bai wawuri kudin gwamnatin da ke karkashinsa ba, “EIMC sun canza yadda abubuwa su ke wakana ne a NDDC, wannan shi ya jawo duk rigimar da ake yi.”

“Abin ban dariya ne; daga ace Naira biliyan 40 ta bace, sai a koma binciken kudin da aka kashe a wajen kundin kasafi. Sai a koma cewa mu biya bashin ‘yan kwangila.”

Ya yi karin haske, “Wannan ba gaskiya ba ne. EIMC ba ta kashe N81.5b ba. Wannan lissafin abin da kwamitin rikon kwarya su ka batar ne tun daga Oktoban 2019 zuwa Mayun 2020.”

“Abin da IMC ta kashe daga Fabrairu zuwa kMayun 2020, shi ne N59.1bn. A cikin wannan, N38.6b, sun tafi wajen biyan ayyukan da ‘yan kwangila su ka yi da bashin da ake binmu."

Pondei wanda ya fuskanci tambayoyi a Majalisar wakilai ya ce binciken kudin da ake yi zai fito da mai gaskiya a ma’aikatar NDDC mai kula da cigaban yankin Neja-Delta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel