Rashin tsaro: El-Rufai zai saka CCTV da jirage marasa matuka a Kaduna

Rashin tsaro: El-Rufai zai saka CCTV da jirage marasa matuka a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatinsa tana saka na'urorin CCTV a yankin kudancin Kaduna, hakan na daga cikin kokarin karfafa tsaro tare da dawo da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan a wata takarda da yasa hannu a ranar Litinin bayan taron da yayi da shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, Rabaren Supo Ayokunle da sauran shugabannin CAN a Kaduna.

Kamar yadda takardar ta bayyana, tun a watan da ya gabata, gwamnatin jihar da jami'an tsaro suke aiki wurin shawo kan rikici da kashe-kashen da suka addabi jihar.

"Muna matukar bakin ciki da rashin rayuka da ke faruwa sakamakon hare-haren da ke aukuwa a yankin.

"A yayin da muke makokin mamata, yanzu abinda za mu mayar da hankali a kai shine hana ci gaban faruwar hakan. Mun mayar da hankali wurin kawo karshen matsalar da ta addabi jihar na sama da shekaru 40.

Rashin tsaro: El-Rufai zai saka CCTV da jirage marasa matuka a Kaduna
Rashin tsaro: El-Rufai zai saka CCTV da jirage marasa matuka a Kaduna Hoto: PM News
Asali: UGC

"Za mu ci gaba da goyon bayan cibiyoyin tsaro na jihar don dawo da zaman lafiya a yankunan. Sama da shekaru biyar da suka gabata, mun zuba kudade a kan fannin tsaro.

"Mun samar da ababen hawa da kayayyakin bukata don goyon bayan hukumomin tsaron da aka turo jihar.

"Za mu saka kimiyyar zamani ta hanyar saka jiragen sama marasa matuka da kuma CCTV a Kaduna, Kafanchan da Zaria."

El-rufai ya kara da cewa, za a duba bukatar da shugaban CAN ya mika gaban shi a tsanake kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Dole ne mu shawo kan rashin tsaro, ko kuma mu fuskanci matsala - Masari

A baya mun ji cewa El-Rufai ya ce gwamnotocin jihar na baya su kan biya wasu shugabanni a kudancin jihar Kaduna da ake zargin suna rura wutar kashe-kashe a yankin.

Gwamnan ya bayyana cewa ba zai biya bukatar 'yan ta'adda ta hanyar basu kudi ba, sai dai ya tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka samu hannunsa a cikin kashe-kashen jama'a a kudancin Kaduna.

Da ya ke magana a wani shirin gidan talabijin na 'Channels', gwamnan ya bayyana cewa gwamnatocin baya na bawa shugabannin yankin kunshin kudi domin kar a samu barkewar rikici.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel