Ghali Na’Abba: Hukumar DSS ta gayyaceni mana nima – Inji Aisha Yesufu

Ghali Na’Abba: Hukumar DSS ta gayyaceni mana nima – Inji Aisha Yesufu

- Aisha Yesufu ta bukaci DSS ta cafketa kamar yadda aka kama wasu kwanan nan

- Yesufu ta nuna sam ba ta jin tsoron ayi ram da ita domin ta shirya juyin juya-hali

- Mai fafutukar ganin an kawo sauyin ta zargi Gwamnatin Buhari da cewa ta gaza

Shararriyar ‘yar gwagwarmayar nan, Aisha Yesufu ta fito ta yi magana bayan ta ji cewa hukumar DSS ta gayyaci Ghali Umar Na’Abba domin amsa wasu tambayoyi.

Aisha Yesufu ta yi magana a shafinta na Twitter, ta ce ina ma ace jami’an DSS masu fararen kaya za su gayyace ta kamar yadda ake gayyatar wasu manya kwanan nan.

Hajiya Aisha Yesufu ta rubuta: “Shin jami’an DSS ba su iya aiko mani gayyata? An bari a rage mani hanya zuwa gida.”

Wannan Baiwar Allah ta soki gwamnati jam’iyyar APC mai-ci, ta ce hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari kan mulki, annoba ne ga Najeriya.

A cewar Aisha Yesufu, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wanda ta karbi mulki a 2015, ta gaza kawo zaman lafiya da tsaron jinane da dukiyoyin al’umma.

“(Buhari) ya gaza, bayan haka kuma ana tafka rashin gaskiya. Mutuwa a Najeriya saboda sakacinsa ta zama ba komai ba.”

KU KARANTA: Janar Zamani Lekwot ya yi magana game da rikicin Kaduna

Ghali Na’Abba: Hukumar DSS ta gayyaceni mana nima – Inji Aisha Yesufu
Aisha Yesufu
Asali: UGC

“A duk lokacin da ni ji an kashe wani, sai in tambayi kai na, ko shin na fi wanda ya mutu ne? Idan na ce mamatan yau su na raye jiya, sai in fahimci cewa wannan lokaci kadai gare ni.”

Yesufu wanda ta na cikin wadanda su ka kafa kungiyar BringBackOurGirls bayan sace ‘yan matan Chibok, ta ce wadanda ke cikin gidan yari sun fi mutanen da ke saki ‘yanci.

Yesufu ta ce: “Su na tunanin na fi samun ‘yanci a nan. Ana soma juyin-juya hali ne a can. Mafi yawan wadanda su ke can, ba za su rasa komai don ace babu su ba."

Rikakkiyar ‘yar adawar kuma maras tsoro ta ke cewa babu abin da shugaban kasan zai iya yi mata.

Har yanzu dai DSS ba su tanka Aisha Yesufu ba, amma sun tsare tsohon shugaban majalisa, Ghali Na’Abba da tsohon mataimakin gwamnan CBN, Obadiah Mailafia.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel