Buhari ya ja kunnen 'yan Najeriya a kan tada tarzoma

Buhari ya ja kunnen 'yan Najeriya a kan tada tarzoma

- Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jan kunnen 'yan siyasar Najeriya a zaben gwamnan jihar Edo da ke zuwa da su kiyaye duk wani abu da zai tada tarzoma

- Adams Oshiomhole, tsohon shugaban APC na kasa ne ya sanar da hakan bayan wata ganawar sirri da ya yi da shugaban kasar

- Ya jadadda cewar shugaban kasar mutum ne mai son ganin an mutunta ra'ayin masu zabe, ba wai a tursasa su kan abunda basa so ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jan kunnen 'yan siyasar Najeriya a zaben gwamnan jihar Edo da ke zuwa da su kiyaye duk wani abu da zai tarwatsa dokokin siyasa.

Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron sirri da yayi da shugaban kasa a fadarsa da ke Abuja.

"Na yi masa bayanin abinda ke faruwa. Kun san halinsa a bayyane yake a koda yaushe yana mutunta ra'ayin masu kada kuri'a. Dole ne a kiyaye hakkinsu, kuma ba a amince kowa ya yi amfani da makami ko tashin hankali ba wurin tirsasa masu zaben."

Oshiomhole ya tuna cewa a lokacin da yake shugaban kungiyar kwadago ta kasa, "Yan sanda sau da yawa sun taba harbi tare da kashe min magoya bayana. Ban taba cewa su mayar da martani ga 'yan sanda ba.

Buhari ya ja kunnen 'yan Najeriya a kan tada tarzoma
Buhari ya ja kunnen 'yan Najeriya a kan tada tarzoma Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Na yi zabe kusan sau uku kuma babu tashin hankali. Toh babu abinda zai canza kuma.

"Abu daya da ya sauya, shine gwamnan wanda yake takamar yana da kariya da sauransu.

"Shugaban kasar zai yi farin ciki idan aka yi zabe na gaskiya ba tare da rikici ba kuma babu makamai.

"Kotu tana nan, 'yan sanda kuma za su yi aikinsu. Ba za a duba wacce jam'iyyar bace, doka duk daya ce."

A kan zargin cewa yana son komawa shugabancin APC, Oshiomhole ya ce baya da niyyar sake takarar shugabancin jam'iyyar.

KU KARANTA KUMA: Oshiomhole ya zargi gwamnonin APC da kokarin kai shi kasa

Ya kara da cewa, babban abinda yasa gaba a yanzu shine yakin neman zaben gwamnan APC na Edo, jaridar The Nation ta ruwaito.

"Kun gani, abinda nake so kafafen yada labarai su sani shine, ko a lokacin da aka cire ni a matsayin shugaban APC na kasa, Edo tana APC. Ba wai bani da aikin yi bane. Shekaruna 68 a duniya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel