Mutuwar Janar Iliya: Buhari ya yi alhini, ya aika sako zuwa rundunar soji

Mutuwar Janar Iliya: Buhari ya yi alhini, ya aika sako zuwa rundunar soji

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika sakon ta'aziyya zuwa ga iyali da rundunar soji bisa mutuwar Manjo Janar Samaila Iliya.

A cikin wani jawabi da ya fitar ta bakin kakakinsa, Femi Adesina, Buhari ya bayyana janar Iliya a matsayin mutunin da ya sadaukar da rayuwarsa domin hidimtawa kasarsa kafin ya yi ritaya.

Kazalika, shugaba Buhari ya sake mika sakon ta'aziyya ga abokan marigayin, wanda ya bayyana a matsayin wanda ya kasance shugaba abin koyi a lokacin da ya rike mukamai ma su yawa a rudnunar soji.

Buhari ya yi waiwaye a kan irin nasarar da janar Iliya ya samu a lokacin da ya jagoranci tawagar sojojin Najeriya da aka tura domin tabbatar da zaman lafiya a Rwamda da Lebanon.

A cewar Buhari, jarumtar janar Iliya ta sa an nada shi jagorantar tawagar rundunar sojojin kasashen duniya da majalisar dinkin duniya ta tura jamhiriyar Domokradiyyar Kongo (DR Congo) domin tabbatar da zaman lafiya.

Mutuwar Janar Iliya: Buhari ya yi alhini, ya aika sako zuwa rundunar soji
Buhari
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya yi addu'arc Allah ya ji kansa, ya bawa iyalinsa hakurin jure rashinsa.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, kun samu rahoton cewa Wata babbar kotun majistare da ke Minna, babban birnin jihar Neja, ta zartar da hukuncin daurin shekaru 22 a kan wasu malaman Islamiyya biyu; Hassan Bilyaminu da Abdullahi Bilyaminu.

DUBA WANNAN: Babu ruwan Buhari: Masari ya fadi ma su laifi a matsalar rashin tsaro a Katsina

An gurfanar da malaman biyu 'yan uwan juna a gaban kotu bisa tuhumarsu da aikata fyade a a kan kananan yara guda hudu da ke karatu makarantar Islamiyyarsu.

Babbar alkaliyar kotun, Hauwa Baba Yusuf, ta yanke hukunci a kan tuhuma biyu; cin zarafin kanan yara mata da rashin da'a, da ake yi wa Malaman biyu.

A makon jiya ne rundunar 'yan sandan jihar Neja ta yi bajakolin malaman biyu; Bilyaminu, mai shekaru 25 da dan uwansa; Abdullahi, mai shekaru 23, wadanda dukkansu malamai ne da ke koyarwa a makarantar tsangayar Mallam Bilya da ke Tudun Natsira Maitumbi a Minna.

Dan sanda mai gabatar da kara, Saja Bello Mohammed, ya bayyana cewa an tanadi hukuncin laifukan da Malaman suka aikata a karkashin sashe na 285 na kundin 'penal code' da sashe na 19 (2) na kundin hakkin yara na jihar Neja da aka samar a shekarar 2010.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng