Babu ruwan Buhari: Masari ya fadi ma su laifi a matsalar rashin tsaro a Katsina
Gwamna jihar Katsina Aminu Masari a ranar Lahadi ya wanke shugaba Muhammadu Buhari daga zargin barin tabarbarewar tsaro a jiharsa da kuma Arewa maso Yamma, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.
Shugaban kasa ya yi duk mai yiyuwa don dai daita lamura a shiyyar, a cewarsa, yana mai nuni da cewa rundunar soji ne suka gaza amfani da kokarin shugaban kasar wajen cimma nasara.
Masari ya bayyana hakan ne a taron raba tallafin miliyan goma ga mata 1,000 da kuma tallafin karatu na miliyan bakwai ga dalibai 701 daga karamar hukumar Rimi.
Tallafin makudan kudaden yazo ne daga hannun Salisu Mamman Kadandani, wani mai jin kan al'umma a jihar.
Masari ya kara da cewa 'yan ta'addan a yanzu na rayuwa ne cikin al'umma.
"Mun sansu, mun san iyayensu. Gano dan ta'adda a cikin gari ba wani abu mai wahala bane saboda kasan sana'arsa, girman gonarsa da yawan dabbobinsa," a cewarsa.
"Idan har rana tsaka ya sayi babur na sama da N200,000, to daga nan kasan cewa yana sayar da rayukan mutane ne."
KARANTA WANNAN: 'Ina da hujjoji na yadda aka yi sama da fadi da N6.25bn da aka turawa NDDC na tallafin COVID-19'
A wani labarin; malamin cocin Abuja, Most Rev. Ignatius Kaigama ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna dasu kawo karshen kashe kashe a jihar Kaduna.
Ya yi nuni da cewa yin sulhu da baki, zai fi alkairi fiye da amfani da bindigogi, bama bamai ko kibau.
Kaigama ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da wasu manyan malaman coci guda bakwai a cocin 'Our Lady Queen of Nigeria Pro-Cathedral', Abuja.
"Yin sulhu da baki zai fi magance matsaloli fiye da amfani da bindiga, bam ko kibiya. Muna kira ga gwamnati a dukkan matakai da su kawo karshen kashe kashen da aka yi."
Shugaban kungiyar kiristoci a Nigeria (CAN), Rev. Dr Supo Ayokunle a ranar Lahadi ya bukaci sauran kiristoci da su ci gaba da yin addu'o'i da zanga zangar kin amincewa da kashe kashen da ake yi a Kudancin Kaduna.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng