Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin binciken Kwankwaso

Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin binciken Kwankwaso

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti don binciken wani aikin titi mai tsawon kilomita biyar da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bada. Titin ya ratsa kananan hukumomi 44 na jihar.

Hakazalika, gwamnatin jihar ta amince da dakile kwangilar miliyoyin naira da ta bada a Dawakin Tofa, wanda ta bai wa Messrs CCECC Nigeria Limited a kan N651, 844, 966.51

An bada kwangilar ne a 2012 amma an tsaya da aikin bayan da aka kai rabinsa, lamarin da ya janyo matsi da tsanani a yankin.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ne ya bayyana hakan yayin jawabi ga manema labarai a kan abinda suka tattauna a gidan gwamnatin.

Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin binciken Kwankwaso
Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin binciken Kwankwaso Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Garba ya ce majalisar ta kafa wani kwamitin don bincikar aikin titi na kilomita biyar a kananan hukumomi 44 na jihar.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin kasa a 2023: Matasan Ohanaeze sun bayyana mutum 2 da suka zaba

Ya ce wannan matakin na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na dubawa, kammalawa ko kuma dakatar da duk wata kwangila.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Ganduje ya faɗa wa shugaban hukumar sauraron ƙorafin jama'a da yaƙi da rashawa ta jihar, Muhyi Rimingado ya yi aikinsa ba tare da sani ko sabo ba.

Ganduje ya kuma fada wa Ramingado kada ya ɗaga wa kowa ƙafa wurin yaƙi da rashawa ko da ƴan fadar gwamna ne.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyara hedkwatar hukumar a ranar Asabar domin duba aikin gyara da kwaskwarima da ake yi.

A cewar Ganduje, ba zai yi wu gwamnatin tarayya ita kaɗai ta yi yaƙi da rashawa ba idan jihohi ba za su yi yaƙi da rashawar ba suma.

"Duk wanda ya faɗa tarkon hukumar zai fuskanci hukunci. Ba ruwa na. Ba zan saka baki ba koda wanene. Saboda haka kada ka ɗaga wa kowa ƙafa ko da ƴan fada na ne," a cewar Ganduje.

Da ya ke jawabin buɗe taron tunda farko, Ramingado ya yaba wa ƙoƙarin Ganduje wurin yaƙi da rashawa a jihar inda ya ce," jajircewar ka da goyon baya ne yasa hukumar mu ke cikin wadanda suka fi inganci a jihar."

"Mun zama abin koyi ga wasu jihohi a kasar nan," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel