Hakimin Garin Kufana, Titus Dauda ya kamu da COVID-19

Hakimin Garin Kufana, Titus Dauda ya kamu da COVID-19

- Rahotanni sun tabbatar da cewa Hakimin Kufana ya kamu da COVID-19

- Mista Titus Dauda ya roki mutane su yi masa addu’a yayin da ya ke jinya

- Yanzu haka Basaraken ya na killace a dakin kula da masu Coronavirus

Rahotanni sun ce an tabbatar da cewa Hakimin garin Kufana a kasar Kajuru, jihar Kaduna, Mista Titus Dauda ya kamu da cutar COVID-19.

Daily Trust ce ta fitar da rahoto cewa Titus Dauda ya na dauke da kwayar cutar COVID-19. An tabbatar da wannan ne a ranar 17 ga watan Agusta, 2020.

Jaridar ta ce tun kafin yanzu, Titus Dauda ya na ta fama da zazzabi. A dalilin haka ne aka garzaya da shi zuwa wani asibiti a makon da ya wuce.

A asibitin ne aka tabbatar da cewa Hakimin na Kufana ya kamu da cutar COVID-19. Wannan Basarake ya shiga sahun wadanda annobar ta kwantar a Kaduna.

A wani jawabi da ya fito daga fadar hakimin a ranar Asabar, ya bayyanawa Duniya cewa ya na dauke da kwayar COVID-19 mai jawo wahalar numfashi.

KU KARANTA: COVID-19 ta kashe mutum 3 a Kaduna

Hakimin Garin Kufana, Titus Dauda ya kamu da COVID-19
Gwamnan Kaduna ya yi jinyar COVID-19 a baya Hoto: Twitter
Asali: Facebook

Wannan jawabi ya na cewa: “Fiye da mako guda kenan ina fama da zazzabi, sai aka kai ni asibiti domin ayi mani magani.”

Fadar Hakimin ta tabbatar da abin da ake tsoro, ta ce Titus Dauda ya na da COVID-19, yanzu haka ya na jinya kamar yadda hukumomi su ka tanada.

“Sai na zabi in yi gwajin ciwon COVID-19, sakamakon ya kuma fito a ranar Asabar, 15 ga watan Agusta, 2020, an gano ina dauke da kwayar cutar.”

“Yanzu haka ina dakin gwamnati na killace masu COVID-19, ana kula da ni, kuma ina cikin yanayi mai kyau.”

Jawabin Hakimin ya kare da barar addua’, ya ce, “Ina rokonku duka ku sani da sauran wadanda mu ke dauke da wannan ciwo a addu’o’inku.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel