Yanzu-yanzu: DSS ta sake gayyatar Mailafia

Yanzu-yanzu: DSS ta sake gayyatar Mailafia

- Hukumar DSS ta sake gayyatar tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailafiya, don sake amsa tambayoyi

- DSS na tsammanin zuwan Mailafiya ofishinsu na jihar Filato wurin karfe 12:00 na rana a yau Litinin, 17 ga watan Augustan 2020

- Da farko dai Mailafiya ya amsa gayyatar DSS a Jos kan tattaunawa da yayi da wani gidan rediyo inda ya zargi wani gwamnan arewa da zama kwamandan Boko Haram

Hukumar jami'an tsaro ta farin kaya, ta sake gayyatar tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailafiya, don sake amsa tambayoyi.

Jaridar The Nation ta gano cewa, DSS na tsammanin zuwan Mailafiya ofishinsu na jihar Filato wurin karfe 12:00 na rana a yau Litinin, 17 ga watan Augustan 2020.

Lauyansa, Bawa Ba Esq, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a waya.

Barista Bawa ya sanar da The Nation a safiyar Litinin cewa, ci gaban tattaunawar da suka fara da jami'an ne za su ci gaba.

Yanzu-yanzu: DSS ta sake gayyatar Mailafia
Yanzu-yanzu: DSS ta sake gayyatar Mailafia Hoto: Punch
Asali: UGC

A kan dalilin sake gayyatar, Bawa ya yarda cewa ba wani sabon abu bane daban da waccan gayyatar da aka taba yi masa.

A ranar Laraba da ta gabata, Mailafiya ya amsa gayyatar DSS a ofishinsu a Jos a kan wata tattaunawa da yayi da wani gidan rediyo inda ya zargi wani gwamnan arewa da zama kwamandan Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Fadar shugaban kasa ta yi martani

Mailafiya ya amsa tambayoyin DSS na tsawon sa'o'i shida a ofishinsu.

An yi yunkurin tattaunawa da Obadiah amma ba a samu dama ba, don baya daukar wayarsa kuma bai yi martani a kan sakon da aka tura masa ba.

A baya mun ji cewa hukumar DSS, a ranar Juma'a ta caccaki tsohon mataimakin gwamnan CBN, Dr Obadiah Mailafiya, inda ta siffantashi matsayin makaryaci kuma mai yada labaran bogi.

DSS, ta bayyana hakan ne a takardar da kakakinta, Peter Afunanya, ya rattafa hannu inda tace ta ji kunya mutum irin Obadiah Mailafiya wanda ke da alaka da manyan ma'aikatan gwamnati da zai iya fadawa bayanin da ya samu amma ya zabi wuce gona da iri.

Hukumar ta ce lokacin da yake ofishinsu dake Jos, ya karyata maganar da yayi amma da ya samu yanci sai ya fara cewa yana kan bakansa, Vanguard ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel