Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Fadar shugaban kasa ta yi martani

Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Fadar shugaban kasa ta yi martani

- Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan gayyatar Na'Abba da hukumar tsaro ta farin kaya ta yi

- Ta ce ba caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari bane ya sa hukumar tsaron ta gayyaci tsohon kakakin majalisar ba

- Tsohon kakakin majalisar wakilan dai ya ce DSS ta gayyacesa ne saboda kalubalantar mulkin Buhari da yayi

Fadar shugaban kasa ta ce miyagun tsokacin da ake zargin Ghali Na'Abba da su, ba su bane suka janyo hankalin hukumar jami'an tsaro ta farin kaya har da suka gayyacesa.

A wata takarda da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a Abuja a daren Lahadi, ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da labaran da ake yadawa na cewa an gayyacesa a kan caccakar Buhari.

A cikin ranakun karshen makon nan ne tsohon kakakin majalisar wakilai ya ce DSS ta gayyacesa ne saboda kalubalantar mulkin Buhari da yayi, jaridar Tribune ta ruwaito.

Kamar yadda takardar ta ce: "fadar shugaban kasa na kira ga jama'a da su yi watsi da labaran da ke yawo a kan cewa DSS ta gayyaci Umar Ghali Na'Abba a kan tsokacin da yayi a kan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Fadar shugaban kasa ta yi martani
Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Fadar shugaban kasa ta yi martani Hoto: Politicsnigeria.com/ Thewhistler.ng
Asali: UGC

"Binciken mu ya nuna cewa, gayyatarsa da suka yi bata da alaka da abinda yace kuma hakan bai kai ga hankalin fadar shugaban kasa ko wasu 'yan siyasa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya aika sakon gaisuwa ga Babangida yayinda ya cika shekaru 79 a duniya

"Akwai manyan 'yan siyasa da ke magana kuma fadar shugaban kasa na mayar da martani. Ko wadanda ke shirya karyayyaki na siyasa basu damun fadar shugaban kasar.

"Muna shawartar Na'Abba da su nisanta fadar shugaban kasar daga halin da ya tsinci kansa kuma ya fitar da kansa yadda ya dace."

A baya mun ji cewa Ghali Umar Na'Abba, ya tabbatar da cewa zai amsa gayyatar hukumar DS a babban ofishinsu da ke Abuja a ranar Litinin, karfe 12 na rana a kan tattaunawar da yayi da wani gidan talabijin a makon da ya gabata.

Na'abba ya yi tattaunawar ne a matsayinsa na daya daga cikin shugaban wata kungiya mai suna NCF.

A takardar da shugaban fannin yada labarai na kungiyar, Dr. Tanko Yunusa ya fitar, ya ce Na'Abba zai amsa gayyatar, duk da kuwa ya ce a hankali kasar ke barin salon mulkin farar hula.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel