Mazauna Abuja sun koka a kan yawan sace-sacen mutane
- Wasu yankuna a babbar birnin tarayya na fuskantar yawan garkuwa da mutane
- Mazauna yankunan sun ce a yanzu su kan koma gidajensu kafin karfe 7:00 na yamma saboda ayyukan wasu ‘yan bindiga da ba a sani ba
- Sun kuma yi korafin cewa jami’an ‘yan sanda da ke tsaron unguwanni da dama basu isa ba
Wani rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa wasu mazauna yankin Life Camp da ke babbar birnin tarayya, Abuja sun koka kan hauhawan yawan garkuwa da mutane a yankin.
Mafi akasarin mazauna unguwannin Menreng, Winning Clause, Canaan, Dabo Lias, Kingstown da Katsina duk a yanki guda na korafi.
A cewar mazaunan, a yanzu su kan koma gidajensu ne kafin karfe 7:00 na yamma domin tsoron kada ‘yan bindiga su yi gaba da su.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar unguwannin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce biyu daga cikin wadanda abun ya cika da su na zama ne a Estate din Katsina.

Asali: UGC
Ya ce ‘yan bindigan na amfani da damar wani kwana mai zurfi da jeji tsakanin Dabo da unguwan Katsina wajen farma mazauna, sannan su yi ta harbin motocinsu wanda hakan kan tursasa su tsayawa sannan su kuma su sace su.
Ya ce: “Mun samu lamarin guda biyu, daya kimanin wata guda da ya gabata, an yi garkuwa da daya daga cikinmu kuma mun biya fansa kafin all sake shi.
KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Abubuwa 3 da suka hana cutar yin tasiri a Afrika
“Yana hanyar zuwa unguwarsa da misalin karfe 11:00 na dare. Ya ga wasu ‘yan bindiga su takwas a wajen sannan suka fara harbinsa, ya tsaya sai suka yi garkuwa da shi.”
Ya ce ofishin yan sanda mafi kusa shine a Life Camp amma ya yi korafin cewa akwai karancinsu a unguwannin.
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne sun kai farmaki wani kauye a jihar Yobe.
Maharan sun shiga garin Mashio da ke karamar hukumar Fune sannan suka fara harbi ba kakkautawa, inda suka sace hakimin kauyen, Isa Mai Buba da dansa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, da kuma mukaddashin shugaban karamar hukumar da abun ya shafa, Abubakar Kolere sun tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talbijin din Channels.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng