An cafke wani mutum da ake zargi da luwadi da kanan yara 12 a Sokoto

An cafke wani mutum da ake zargi da luwadi da kanan yara 12 a Sokoto

- Hukumar NAPTIP ta cafke wani lebura mai suna Lawali Bala wanda ke zama a kauyen Rikina na karama Dange/Shuni, jihar Sokoto

- Ana zargin Lawali da aikata luwadi da wasu kananan yara har su 12

- An tattaro cewa ya kan bi dukkanin yaran zuwa inda suke kwance sannan ya tattaro su zuwa inda yake ya yi luwadi da su

Hukumar yaki da safarar mutane ta kasa (NAPTIP) ta damke wani lebura mai suna Lawali Bala wanda ke zama a kauyen Rikina na karama Dange/Shuni, jihar Sokoto bisa zargin luwadi da wasu yara kanana har 12.

An dai gano cewa Lawali na luwadi da yaran maza har su 12 idan iyayen yaran suka yi barci da daddare.

Darektan hukumar NAPTIP reshen jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi, Mitika Mafa-Ali, ya bayyana haka da yake hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya, a garin Sokoto.

An cafke wani mutum da ake zargi da luwadi da kanan yara 12 a Sokoto
An cafke wani mutum da ake zargi da luwadi da kanan yara 12 a Sokoto Hoto: Punch
Asali: UGC

Ali yace wannan Lebura na aiki ne a karkashin iyayen wadannan yara. “A haka ne ya rika yin fasikanci da yaran maza sannan yana koya musu dabi’ar yin luwadi a lokacin da iyayen su ke barci."

An tattaro da cewa yakan lallaba bi dukkanin yaran su 12 zuwa inda suke kwance sannan ya tattaro su zuwa inda yake domin ya yi luwadin da su.

KU KARANTA KUMA: Dakatar da sarakuna a kan ziyartar Buhari: Basarake ya yi martani ga gwamnan PDP

Da yake magana yayinda yake tsare, Bala ya ce ya zo kauyen Rikina daga Zamfara sannan sai iyayen yaran suka bashi masauki.

Wanda ake zargin ya tabbatar da cewar yana luwadi da yaran domin mafi akasarin lokuta tare suke bacci da daddare.

Ya daura laifin a kan sharrin shaidan, inda ya kara da cewar wani mutum a jihar Neja ne ya koya masa luwadi inda shi kuma ya ci gaba da aikatawa domin jin dadinsa.

Daya daga cikin yaran da abun ya cika dasu ya fada ma NAN cewa shekarunsa 14 kuma yana a aji hudu a makarantar firamare na Rikina.

Ya ce wanda ake zargin na binsu wajen bacinsu ne.

Daya daga cikin iyayen yaran ya bayyana cewa an taba kai karar shi ofishin Hisbah kafin a dangana ga sanar da hukumar NAPTIP abinda yake yi, har suka damke shi.

A wani labarin kuma, wata kotun majistare ta hudu da ke zama a Birnin Kebbi, ta bukaci a adana mata wani ma’aikacin banki mai suna Hussaini Sahabi a gidan gyara hali.

Ana zargin matashin mai shekaru 25 da yin luwadi da wani yaro mai shekaru 10, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda aka shigar da karar, an zargi matashin mai aiki da wani banki a jihar da lalata karamin yaron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel