Dakatar da sarakuna a kan ziyartar Buhari: Basarake ya yi martani ga gwamnan PDP

Dakatar da sarakuna a kan ziyartar Buhari: Basarake ya yi martani ga gwamnan PDP

Daya daga cikin sarakunan gargajiya 12 da Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya dakatar, ya ce ya yi kuskure tare da fatan gwamnan ya yafe masa.

Igwe MacAnthony Okonkwo na yankin Alor a karamar hukumar Idemili ta jihar Anambra, ya fito ya bai wa Obiano tare da majalisar sarakunan jihar hakuri a kan take wasu dokokin masarautun jihar da yayi.

Amma sauran sun jaddada cewa gwamnan bashi da damar shiga wannan hurumin.

A ranar Juma'a ne Obiano ya sanar da dakatar da sarakuna 12 a jihar sakamakon ziyarar da suka kai wa Buhari a Abuja.

Okonkwo na Alor, yana daya daga cikin sarakuna 12 da aka dakatar na tsawon shekara daya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Dakatar da sarakuna a kan ziyartar Buhari: Basarake ya yi martani ga gwamnan PDP
Dakatar da sarakuna a kan ziyartar Buhari: Basarake ya yi martani ga gwamnan PDP Hoto: PM News
Asali: Facebook

Umarnin dakatarwar na kunshe ne a wata takarda da kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya na jihar, Greg Obi, yasa hannu.

Takardar ta ce an dakatar da sarakunan ne sakamakon tafiyar da suka yi wajen jihar ba tare da amincewar gwamnati ba.

Amma a yayin martani a karshen makon nan yayin zantawa da manema labarai, Along ya ce ya yi ba daidai ba kuma yana mika ban hakurinsa ga Obiano.

Ya ce, "babban kuskure ne a bangaren da ban sanar da gwamnatin ba cewa za mu je Abuja. A don haka nake mika ban hakuri."

Okonkwo ya musanta rade-radin da ake yi na cewa an hada shi da kudin tare da wasu kyautuka kafin ya amince ya raka Yarima Eze ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce kudin da aka ga yana kirgawa na direbansa ne da wasu hadimansa. Ya ce bai san yadda za a yi mutum mai daraja kamarsa zai karba cin hanci ba.

KU KARANTA KUMA: Ku daura laifin rashin tsaro a kan shugabannin tsaro - Gwamna Masari

"Ta yaya za su kira shi cin hanci? Wanne irin cin hanci ne? Wannan karya ce kawai. Ina kirgawa direban da sauran hadimai na kudin mai da sauran abubuwan bukata ne.

"Ban taba karbar cin hanci daga kowa ba a rayuwarta. Amma idan ana so in karba, sai dai a cika min babbar jakar 'Ghana Must Go' 10 zuwa 20 da daloli. Daga nan sai a fara magana."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel