Hukuncin kisa a kan batanci: CAN ta bayyana matsayarta

Hukuncin kisa a kan batanci: CAN ta bayyana matsayarta

A ranar Litinin da ta gabata ne wata kotun shari'ar Musulunci ta yankewa wani matashi mai suna Sharif-Aminu hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon batanci da ya yi ga Annabi Muhammadu.

Duk da matashin yana da kwanaki 30 don daukaka karar matukar bai gamsu da hukuncin ba, shugaban majalisar malamai, Sheikh Muhammad Nasir Adam, ya ce gwamnati ta gaggauta saka hannu a kan hukuncin kotun ba tare da duban siyasa ba.

Adam, wanda ya zanta da manema labarai a Kano, ya jinjinawa kotun da ta yanke wannan hukuncin kuma ya ce hakan ne Musulunci ya tanadar.

Hukuncin kisa a kan batanci: CAN ta bayyana matsayarta
Hukuncin kisa a kan batanci: CAN ta bayyana matsayarta
Asali: Twitter

Malamin ya yi bayanin cewa Musulunci addini ne mai son zaman lafiya amma ya gindaya yadda rayuwa ya kamata ya tafi.

Ya ja kunnen masu caccakar hukuncin da su guji yin hakan saboda yana iya kawo rashin zaman lafiya a kasar.

Hakazalika, babban limamin masallacin Sheikh Muhammad Ja'afar Adam da ke Sabuwar Gandu, Sheikh Abdullahi Gargamawa, ya yi kira ga Ganduje da ya amince da hukuncin kisa a kan Sharif ba tare da jinkiri ba.

Gargamawa, wanda ya yi magana a kan hukuncin a hudubar sallar Juma'a da ta gabata, ya ce gwamnati ta dage tare da jurewa wurin zartar da hukuncin shari'a.

Limamin ya kawo misalai daga ayoyi da hadisai inda ya ce wannan hukuncin ya yi daidai a kan Sharif.

A martanin shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Adeolu Samuel Adeyemo, ya ce batanci a addinin Kirista laifi ne da ba a taba yafe shi kuma babu kirita nagari da ya dace ya aikata don karantsaye ne ga dokokin Ubangiji.

Duk da shugaban CAN ya ce wannan hukuncin na Shari'a ne ta Musulunci, ya ce dole ne a jaddada shi idan ana neman zaman lafiya a tsakanin al'umma.

"Mu a CAN, wannan hukuncin na Shari'a ne kuma an bi dokokin Musulunci ne. Don haka ba mu da tacewa saboda matsayar Musulunci ce.

"Shigar mu lamarin bashi da amfani. Amma idan ana son sanin hukuncin batanci a addinin Kirista, toh za mu ce laifi ne mai girma wanda ba a yafewa. Wannan ce matsayar addinin kirista," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel