NCDMB: Buhari ya bude katafaren ginin bene mai hawa 17 a Bayelsa (Hotuna)
- Shugaba Muhammadu Buhari ya jadadda cewa gwamnatinsa za ta cigaba da bawa aiyukan raya kasa muhimmanci
- Buhari ya ce zai cigaba da kamfanonin cikin gida kwagilolin aiyuka domin samar da aiyuka ga dubban 'yan Najeriya
- Ya bayyana hakan ne yayin bude katafaren ginin wata cibiyar sabuwar hukumar gwamnati; NCDMB
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da bawa aiyukan raya kasa muhimmanci.
Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da kamfanonin cikin gida kwagilolin aiyuka.
A cewar shugaba Buhari, yin hakan zai samar da aiyuka ga dubban 'yan Najeriya.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin bude katafaren ginin wata cibiyar sabuwar hukumar gwamnati; NCDMB (Nigerian Content Development and Monitoring Board), a Yenagoa, jihar Bayelsa.
"Wannan ginin bene mai tarihi, mai hawa 17, ya kasance daya daga cikin manyan aiyuka da wannan gwamnati ta yi domin kirkirar aiyuka da ma su saka hannun jari.
"Akwai cibiyar samar da wuta mai karfin 1megawatts da Kuma dakin taro na zamani mai cin mutane 1000.
"Kaddamar da wannan katafaren aiki ya nuna cewa gwamnatinmu ta kafa tarihi a yankin kudu ma so kudu mai arzikin man fetur.
KU KARANTA KUMA: DHQ ta tura rundunonin tsaro na musamman zuwa kudancin Kaduna
"An yi facaka da kudadenku a baya ba tare da yi mu ku wasu aiyuka ba. Ina tabbatar mu ku cewa wasu manyan aiyukan na nan tafe," a cewar Buhari yayin taron bude ginin wanda ya halarta ta yanar gizo.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng