Mayakan Boko Haram sun tare hanya suna yi wa matafiya fashi a kusa a Maiduguri

Mayakan Boko Haram sun tare hanya suna yi wa matafiya fashi a kusa a Maiduguri

- Ƴan ta'addan kungiyar Boko Haram sun tare titi suna yi wa matafiya fashi a kusa da Maiduguri babban birnin jihar Borno

- Rahotanni sun ce ƴan ta'addan ba su shiga cikin gari ba kuma ba su harbi kowa ba kawai kuɗi suke karba

- Daga bisani wasu daga cikinsu sun tafi amma wasu sun cigaba da fashin a wajen Maiduguri nisar kilomita 40 daga babban birnin jihar Borno

Ƴan ta'addan kungiyar Boko a ranar Talata sun kafa shinge suka kuma rika yi wa matafiya fashi a hanyar Maiduguri zuwa Magumeri kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban mafarauta a jihar, Bunu Bukar, ya ce, "Maharan ba su shiga garin kuma ba su harbi kowa ba; kuma a wajen gari kawai suka tsaya suna tare motoccin da ke shiga da fita.

Mayakan Boko Haram sun tare hanya suna yi wa matafiya fashi a kusa a Maiduguri
Mayakan Boko Haram sun tare hanya suna yi wa matafiya fashi a kusa a Maiduguri
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: A shirye na ke in ba da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS ta sako shi

"A zuwa yammacin jiya Talata, wasu daga cikin maharan sun tafi amma wasu suna nan, kimanin kilomita 40 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno - suna tare motocci suna yi wa fasinjoji fashi."

A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun harbe wani Nasiru Aliyu mai shekaru 37 har lahira a garin Gidangizo da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Mazauna garin sun ce ƴ a bindigan sun kuma raunatta mutane hudu kuma suka yi awon gaba da wasu mata biyu ƴaya da ƙanwa; Amina Mudi, 23 da Zainaru, 20.

Rahotonni sun ce ƴan bindigan sun isa garin Gidangizo ne a kan babura misalin ƙarfe 12.30 na dare suka rika bi gida-gida suna neman abinci da kuɗi.

An kashe Aliyu ne yayin da ƴan bindigan suka shiga gidansa suka nemi ya basu kuɗi amma ya ce ba shi da kuɗi.

Mazauna garin sun kuma ce yan bindigan sun yi kutse gidan wani Alhaji Mudi inda suka yi awon gaba da ƴan uwansa biyu; Amina da Zainaru.

Ɗaya daga cikin mazauna garin ya ce, "Ƴan bindigan sun ɗara 12 kuma dukkansu da bindigunsu. A kan babura suka zo; sun kashe Aliyu saboda ya yi jayayya da su cewa ba shi da kuɗi a lokacin da suka nemi ya basu kuɗi.

"Sun masa harbi na kusa. Ƴan bindigan gida-gida suka rika bi. A gidan Alhaji Mudi, sun yi awon gaba da ƴaƴansa mata biyu. Yan bindigan sun raunata mutane da dama."

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel