Wani Likita ya ce burodi da shayi su na iya yi wa mai juna biyu illa a jiki

Wani Likita ya ce burodi da shayi su na iya yi wa mai juna biyu illa a jiki

- Shararren likitan nan Dr. Olufunmilayo ya ba masu juna biyu muhimmiyar shawara

- Likitan ya bayyana yadda burodi da shayi za su iya yi wa mai ciki da yaronta illa a jiki

- A cewarsa, shan shayi zai iya hana jikin mai ciki daukar wasu sinadarai masu amfani

Wani likita ‘dan Najeriya da ke kasar waje, ya bayyana cewa idan mace ta na da ciki, kuma ta na yawan shan shayi ko kuma cin burodi, ta na cikin hadari.

Dr Olufunmilayo ya ce shayi da burodi su kan zama illa a jikin mutum ta yadda za su hana shi daukar sinadarin ‘Iron’ wanda ya ke taimaka lafiyar ‘dan Adam.

Olufunmilayo ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Twiter kamar yadda ya saba fadakar da jama’a. Wannan karo karatunsa ya je ne ga masu iyali ko ma juna biyu.

Ya na da kyau masu ciki su san abubuwan da ya kamata su rika ci ko sha, da kuma abubuwan da bai kamata su rika yin kusa da su ba yayin da cikin na su ya yi nauyi.

KU KARANTA: Yaudara ya raba auren shekara da shekaru a Nairobi

Wani Likita ya ce burodi da shayi su na iya yi wa mai juna biyu illa a jiki
Shayi da burodi su na da illa ga mai ciki
Source: Instagram

Mata su kan yi sha’awar ciye-ciye iri-iri a lokacin da su ka dauki juna-biyu, wannan likita ya nuna wasu daga cikin abubuwan da ake ci su na iya taba lafiyar jariri.

A cewar likitan, rashin ‘Iron’ a jikin mutum zai iya jawo matsaloli da-dama kamar haihuwar kankanin jariri ko ma ta kai an sauka kafin lokacin haihuwa ya iso.

Bugu da kari, likitan ya gargadi masu ciki cewa kwankwadar shayi ya na iya yin sanadiyyar da jariri zai fito babu rai, ko kuma ya koma jim kadan bayan an haife shi.

Da ya ke karin bayani game da juna-biyu, Olufunmilayo ya ce daukar ciki na jawo karancin jini a jikin mace, a dalilin hakane ake nemawa wasu mata sinadarin ‘Iron’.

Shayi da bunu kuwa su na jawo karancin wannan sinadari, musamman ace an hada shayin ne da burodi. Likitan ya ce wannan abinci da aka saba ci, mummunan hadi ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel