Ahmed Musa: Shahararren dan kwallon kafa na Najeriya ya rada wa dansa suna Isa Ahmed Musa

Ahmed Musa: Shahararren dan kwallon kafa na Najeriya ya rada wa dansa suna Isa Ahmed Musa

- Ahmed Musa ya rada wa sabon jaririn da ya haifa suna Isa Ahmed Musa

- Shahararren dan kwallon na kungiyar Super Eagles ya bayyana sunan dan nasa ne a shafinsa na soshiyal midiya

- A yanzu haka Musa na buga wasa a kasar Saudiyya na Al Nassr

Kyafdin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya wato Super Eagles, Ahmed Musa, ya bayyana sunan sabon jinjirinsa a matsayin Isa Ahmed Musa yayinda ya nuna farin cikin zama uba ga wannan da.

Bayan ya rabu da tsohuwar matarsa Jamila, Ahmed Musa ya sake aure, inda ya auri Juliet Ejue a watan Mayun 2017 sannan suka haifi dansu na farko a watan Fabrairun 2018.

Isa da aka haifa a yanzu shine da na hudu a wajen Ahmed Musa domin yana da yara biyu da tsohuwar matarsa.

Ahmed Musa ya je shafin soshiyal midiya domin sanar da labarin mai dadi yayinda ya kuma yi godiya ga Allah da ya sauki matarsa lafiya.

“Yau ya kasance rana na musamman a gareni domin za a rada wa dana suna. Isa Ahmed Musa. Ina addu’an Allah ya sa a ambaci sunanka a wuraren girma kawai.

“Za ka zamo mafita ga al’umman karninka kuma na farko a tsakanin sa’anninka. Ina kaunarka sosai,” Ahmed Musa ya yi bayani.

Ahmed Musa: Shahararren dan kwallon kafa na Najeriya ya rada wa dansa suna Isa Ahmed Musa
Ahmed Musa: Shahararren dan kwallon kafa na Najeriya ya rada wa dansa suna Isa Ahmed Musa Hoto: Ahmed Musa
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Mahaifin yaron da aka daure a turken tumaki ya gurfana a kotu

Musa ya kasance tare da bangaren Al-Nassr na kasar Saudiyya tun a 2018 bayan ya bar Premier League Leicester City.

Ya fara aikinsa ne a makarantar kwallon kafa ta GBS sannan ya buga wa JUTH da Kano Pillars, kungiyoyin kwallon kafa na Najeriya wasa kafin ya tafi Ingila a 2010.

A baya mun kawo maku cewa matar babban ɗan wasar tawagar Super Eagles na Najeriya, Ahmed Musa ta haihu kamar yadda fitaccen ɗan wasar ya sanar a dandalin sada zumunta.

Julie ta haifi ɗa namiji, wannan shine haihuwar ta na biyu tare da ɗan kwallon. A baya ta haifa masa ƴa mace.

Da ya ke sanar da labarin, ɗan kwallon ya mika godiyar sa ga Allah da kuma dukkan wadanda suka taimaka masa da iyalinsa da addu'a.

Ya rubuta;

"Rai kyauta ce daga Allah kuma Allah cikin ikonsa ya bamu kyautar da kuɗi ba za ta iya siya ba. Allah ya bawa iyali na ɗa namiji a safiyar yau... Mahaifiyar ɗan da ɗan duk suna cikin ƙoshin lafiya. Mun gode da addu'a ga goyon baya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel