Nasarori 10 da sojin Najeriya suka samu a kan 'yan bindiga
A ranar Alhamis, rundunar sojin Najeriya ta bayyana nasarorin da ta samu a kan 'yan bindigar daji da suka mamaye yankin arewa maso yamma.
A wata takarda da ta samu sa hannun mukaddashin kakakin rundunar, Bernard Onyeuko, rundunar ta ce Operation Sahel Sanity ta samo shanu kuma ta kama wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a cikin kwanakin da suka gabata.
"Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai ya jinjinawa dakarun a kan zakakurancinsu, nasarori da kuma jajircewarsu," Onyeuko ya ce a takardar.
"Ya yi kira garesu da kada su sassauta. Ya kara da tabbatar wa da jama'ar yankin da cewa dakarun sojin sun shirya bada kariya ga rayuka da kadarori a yankin."
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga sojin da su tsare yankin arewa maso gabas daga 'yan bindiga a yayin da ake kira gareshi da ya sallami shugabannin tsaro.

Asali: Depositphotos
Ga wasu daga cikin nasarorin rundunar:
1. A ranar 5 ga watan Augustan 2020, rundunar da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina ta dakile wani hari da aka shirya kaiwa a kauyen Zamfarawa Kagara.
Bayan shigar 'yan bindigar, dakarun sun isa wajen inda suka yi musayar wuta da su kuma suka kashe daya tare da raunata wasu. An yi nasarar kwato duk shanayen da suka sata.
2. A ranar 6 ga watan Augusta, dakarun da ke Dangulbi sun damke wani wanda ake zargin mai kai wa 'yan bindiga bayani mai suna Rabiu Salish.
An kama wasu mutum biyu da ke siyarwa da 'yan bindigar shanun sata.
3. Hakazalika, rundunar ta samo shanu 17 da aka sace daga kauyen Dogon ruwa.
An samo shanu daga 'yan bindiga wadanda suka tsere bayan rundunar ta isa kauyen bayan bayanan ayyukan da suka samu.
KU KARANTA KUMA: Ahmed Musa: Shahararren dan kwallon kafa na Najeriya ya rada wa dansa suna Isa Ahmed Musa
4. Dakarun da ke sintiri sun damko wani wanda ake zargi yana kai wa 'yan bindiga bayanai da kayan bukata mai suna Saifullahi Adamu a Garin Dodo da ke Katsina.
Matarsa mai suna Hauwa Abubakar ta ce a bisa dole ya aureta sannan abokansa 'yan bindiga na ci mata zarafi bayan da suke zarginta da fallasa al'amuransu.
5. A ranar 7 ga watan Augusta, dakarun da ke Anka yayin sintiri sun damko wasu mutum biyu da ake zarginsu da siyar da shanun sata. Ana ci gaba da bincike a kansu har yanzu.
7. Hakazalika, a ranar 7 ga watan Augusta, rundunar soji da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar ta gaggauta zuwa wurin da aka yi musu kiran gaggawa sakamakon ayyukan 'yan bindigar. Sun bar kayayyakin da suka sata tare da shanu 8 inda suka tsare.
7. A ranar 8 ga Satan Augusta, dakarun sun cafke wani mutum mai suna Sallahu Rabiu a kauyen Natsinta da shanu uki. Ya amsa cewa yana da kungiyarsa ta satar shanu.
8. A ranar 9 ga watan Augusta, dakarun da ke Mara sun kama wasu 'yan bindiga masu suna Jamilu Mai da Aminu Lawal a kusa da titin Danmusa zuwa Runka.
A wannan ranar, yayin sintiri sun damke wani Sani Sa'idu da ke sojan gona da kayan 'yan sanda.
9. A ranar 10 ga watan Augusta, dakarun da ke Yarsanta sun gano wani Auwal Yusuf wanda 'yan bindiga suka sato amma ya tsere.
10. A ranar 12 ga watan Augusta, rundunar sojin da ke Yar Gamji a Batsari yayin sintiri sun damko wani Ibrahim Musa.
A yayin da aka tuhumesa, wanda ake zargin ya amsa cewa shi dan leken asiri ne kuma yana shugabantar wata kungiyar 'yan ta'adda mai suna Danladi Dahiru da ke dajin Dumburum.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng