Mahaifin yaron da aka daure a turken tumaki ya gurfana a kotu
- Mahaifin yaron da aka kafe a turken tumaki a jihar Kebbi, ya gurfana a gaban kotu
- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar
- An kama Aliyu Umaru da laifin zalunci ga dansa
Aliyu Umaru, wanda ya kafe yaro mai shekaru 12 a turken tumaki a jihar Kebbi, ya gurfana a gaban kotu.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, ya bayyana hakan a wata takarda, jaridar The Nation ta ruwaito.
Kamar yadda yace: "Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi na sanar da jama'a cewa a ranar 09/08/2020 ne bayani ya riskemu.
"Cewa wani Jibrin Aliyu mai shekaru 12 da ke yankin Badariya a Birnin Kebbi an daure shi a garken tumaki da kaji na tsawon shekaru biyu bayan rasuwar mahaifiyarsa.
"Bayan samun rahoton, jami'ai da ke hedkwatar 'yan sanda da ke birnin Kebbi sun gaggauta zuwa. Sun ceto shi tare da kai shi asibitin Yahaya da ke Birnin Kebbi don kula da shi.
"A yayin bincike, an gano cewa Jibrin Aliyu yana da wani ciwo kuma mahaifinsa ya tabbatar da cewa ya daure shi da igiya ne saboda ya kai shi wuraren masu maganin gargajiya amma duk babu nasara.
KU KARANTA KUMA: WAEC: Ganduje ya yi afuwa ga daliban kwaleji da suka yi mishi zanga-zanga
"A maimakon mahaifinsa ya ci gaba da yi mishi magani, ya yanke hukuncin barin shi kamar dabba.
"A saboda haka, an kama Aliyu Umaru da laifin zalunci ga dan sa kuma an gurfanar da shi a gaban kotu."
A baya mun ji cewa wata mata ta daure yaro maraya, mai suna Jibril Aliyu, na tsawo shekaru biyu a garken tumaki ba tare da abinci isasshe ba a jihar Kebbi.
Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, matar uban yaron ta dinga yi mishi tamkar ba dan Adam ba bayan rasuwar mahaifiyarsa.
Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani a sa'o'in farko na ranar Litinin, wanda ke nuna yaron a rame har baya iya tashi tsaye saboda yunwa.
Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, an damke wacce ake zargin yayin da aka kwantar da yaron a asibitin tunawa da Yahaya da ke Birnin Kebbi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng