Na ba Omoyele Sowore kwanaki 7 ya fito ya janye maganganun da ya yi game da ni - IGP

Na ba Omoyele Sowore kwanaki 7 ya fito ya janye maganganun da ya yi game da ni - IGP

Sufeta janar na ‘Yan sanda, Mohammed Adamu ya karyata rahotannin da ke yawo na cewa ya na neman kudi domin gina makarantar horas da ‘yan sanda a jihar Nasarawa.

Jaridar Punch ta rahoto Mohammed Adamu ya na cewa zargin ya na neman kudi ta hanyar da ba ta dace ba domin kafa makarantar horas da ‘yan sanda a mahaifarsa ba gaskiya ba ne.

IGP ta bakin wani babban lauya da ya tsaya masa, ya yi wannan jawabi ne ya na mai karyata wani rahoto da ya fito daga gidan jaridar Sahara Reporters a ranar 3 ga watan Agusta, 2020.

Dr. Alex Izinyon (SAN) ya yi maganar shiga kotu da shugaban kamfanin jaridar Sahara Reporters, Mista Omoyele Sowore wanda ya zarga da laifin bata sunan shugaban ‘yan sandan kasar.

Alex Izinyon ya fitar da jawabi mai taken: ‘Re: Defamatory publication against Mr Mohammed Abubakar Adamu, NPM, mni (current Inspector-General of Police): Demand for retraction and unequivocal apology’.

Lauyan ya yi raddi ga rahoton da aka fitar, ya kuma bukaci jaridar da mai kamfaninta da su yi maza su fito ta nemi afuwar shugaban ‘yan sandan kasar, Mohammed Abubakar Adamu.

KU KARANTA: Na shirya ba da rai na fansa a kan Najeriya - inji Mailafia

Na ba Omoyele Sowore kwanaki 7 ya fito ya janye maganganun da ya yi game da ni - IGP
Omoyele Sowore
Asali: UGC

Izinyon ya ce idan har Omoyele Sowore da jaridarsa ba su yi wannan ba, zai maka su a gaban hukumomin gwamnatin Najeriya da ke da alhakin karbowa IGP hakkinsa.

Sufetan ‘yan sandan ta bakin wannan lauya ya ba Sowore kwanaki bakwai ya janye maganganun da ya yi, sannan ya bada hakuri a gidajen jaridu uku na kasar da kuma kamfaninsa.

Muddin Mista Omoyele Sowore ya gaza yin wannan, zai hadu da Mohammed Abubakar a kotu.

Wannan lauya ya ce shugaban ‘yan sandan ya sanar da Sowore cewa babu komai a rahoton da ya fitar a jaridarsa sai tulin karya da sharri da ya yi masa da nufin cin mutunci.

Izinyon SAN ya kare wasikar da cewa: “Ba za mu bata lokacinmu a nan ba, za mu yi tanadi domin lokacin da ya fi dacewa.” Ma'ana za a saurare su a gaban kuliya nan gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel