Sojoji sun tarwatsa matattaran da rumbun 'yan Boko Haram a Yamud

Sojoji sun tarwatsa matattaran da rumbun 'yan Boko Haram a Yamud

Harin da jiragen rundunar sojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole suka kai ya tarwatsa rumbun makaman 'yan ta'addan Boko Haram da ke Yamud a yankin Gulumba Gana Kumshe da ke Borno kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan da dama sun mutu sakamakon harin.

Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar Enenche, a cikin sanarwar da ya fitar ya ce an kai harin ne bayan da aka samu sahihan bayannan sirri.

Sojoji sun tarwatsa matattaran da rumbun 'yan Boko Haram a Yamud
Sojoji sun tarwatsa matattaran da rumbun 'yan Boko Haram a Yamud
Source: UGC

A cewar sanarwar, "Dakarun sama na Operation Lafiya Dole sun lalata dakin ajiyar kayan yan ta'addan kungiyar Boko Haram da ke Yamud kan hanyar Gulumba Gana Kumshe na jihar Borno.

DUBA WANNAN: Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel

"An kai harin ne a jiya 11 ga watan Agustan 2020 bayan samun sahihan bayannan sirri da ke nuna cewa wurin ma'ajiyar 'yan ta'adda ne da suka haduwa kafin su kai hari.

Ta kara da cewa, "An kara amfani da naurar leken asiri inda aka gano yan taaddan da dama a cikin gidan da harabarsa da wasu gidaje da suka amfani da su domin ajiyar kaya da haduwa.

"Hakan yasa dakarun saman suka aike da jiragen yakinsu zuwa wurin inda suka yi nasarar tarwatsa shi kana suka yi nasarar kashe wasu da dama cikin 'yan ta'addan."

A wani rahioton na Legit.ng kun ji cewa shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya zargi dukkan Musulman Najeriya da aikata laifin batanci.

Shekau ya bayyana hakan ne a matsayin martani a kan wasu rahotanni da su ka bayyana cewa ya soki hukuncin kashe matashin mawaki, Yahaya Aminu Sharif, saboda wallafa mai dauke da kalaman batanci a kan annabi Muhammad.

Legit.ng Hausa ta ci karo da kalaman Shekau a shafi tuwita na fitaccen lauyan nan mazaunin Kano, Barista Bulama Bukarti.

A cikin takaitaccen sakon da Bukarti ya wallafa a shafinsa, ya bayyana cewa; "rahoton cewa Shekau ya soki hukuncin kashe mawaki ba gaskiya bane. Sabanin hakan, Shekau ya goyi bayan hukuncin kisan.

"Hasali ma, ya bayar da shawarar a gaggauta kaddamar da hukuncin tare da janye ma sa damar daukaka kara.

"Kazalika, ya zargi dukkan Musulmin Najeriya da aikata laifin batanci," kamma yadda Bukarti ya wallafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel