Hausawan wani yankin kudancin Kaduna sun nemi El-Rufa'i ya yi musu masarauta

Hausawan wani yankin kudancin Kaduna sun nemi El-Rufa'i ya yi musu masarauta

Kungiyar al'umman Hausawa a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya samar musu da masarauta.

Yankin karkashin Cibiyar Na-Tanko, wata kungiyar Hausawa a Chikun sun ce suma sun cancanci samun masarauta kamar na Kajuru, Sanga, Kauru, Kagarko, Zangon Kataf da Lere don samun hadin kai da zaman lafiya.

Shugaban kungiyar, Alhaji Aminu Idris, Turakin Nasarawa, tare da sakataren, Yusuf Muhammad Yunus, sun yi kira ga gwamnatin jihar da tayi kokari wurin samar wa Hausawan yankin masarautarsu.

"Yankin mu zai ci gaba da mika bukatar samar wa Hausawa masarauta a karamar hukumar Chikun kamar sauran kananan hukumomi.

"Muna son sanar da cewa yankinmu da karamar hukumar mu bata taba shiga cikin yanki na uku ba. Chikun na cikin yanki na biyu ne," suka ce.

Hausawan wani yankin kudancin Kaduna sun nemi El-Rufa'i ya yi musu masarauta
Hausawan wani yankin kudancin Kaduna sun nemi El-Rufa'i ya yi musu masarauta Hoto: The Cable
Asali: UGC

Kungiyar ta ce wannan shine abinda doka ta ce, Chikun da Kajuru duka yanki na biyu kuma haka zai ci gaba da kasancewa.

Kungiyar ta kara da jinjinawa kokarin gwamnan jihar Kaduna, Nasir a kan kokarinsa na hada kan yankunan jihar.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kama tsohon da ya sace yarinya yana bada haya don lalata da ita

Sun jinjinawa mulkin Hajiya Hadiza Ladi Yahuza, a kan yadda ta mayar da hankali wurin tabbatar da zaman lafiya a Chikun.

Kungiyar Cibiyar Na-Tanko an kafa ta ne don sake hada kai tare da bada kariya ga yankin Hausawa na Chikun, Daily Trust ta ruwaito.

A wani labarin kuma, Shehu Sani ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saurari shugabannin kudancin Kaduna, ganin cewa zubar da jinin da ake yi ya ki cinyewa.

Tsohon dan majalisar, ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Augusta, a yayin da lamurran 'yan bindiga ke sake tsamari a yankin Kaduna ta kudun.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Sani ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai iya gano gaskiyar lamari da kuma musababbin fadan da ake yi a yankin.

Idan za a tuna, rikici a yankin ya kawo karshen rayukan daruruwan Mutane a yayin da ake ci gaba da kutsawa sauran yankunan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel