Gwamna a arewa ya bukaci FG ta bai wa jama'a damar yawo da makamai

Gwamna a arewa ya bukaci FG ta bai wa jama'a damar yawo da makamai

- Gwamna Samuel Ortom, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bar 'yan kasa masu hankali su dinga yawo da miyagun makamai

- Sai dai Ortom ya ce dole a bi tsarin doka sosai wajen aiwatar da wannan manufar domin gujewa shigar makaman hannun wadanda bai dace ba

- Ya kuma ce akwai bukatar a sakarwa hukumomin tsaro kudi da kuma horar da jami'an tsaron don yakar rashin tsaron

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bar 'yan kasa masu hankali su dinga yawo da miyagun makamai kamar AK47, domin yakar 'yan ta'adda da ke kashe 'yan Najeriya.

Ya ce ya kamata a bi tsarin doka sosai wajen aiwatar da wannan manufar domin gujewa shigar makaman hannun wadanda bai dace ba, Channes TV ta ruwaito.

Wannan na daga cikin abinda ke kunshe a takardar da Gwamna Ortom ya gabata a taron yanar gizo da aka yi na cibiyar shugabanci tare da hadin guiwar kungiyar gwamnonin Najeriya.

Gwamna a arewa ya bukaci FG ta bai wa jama'a damar yawo da makamai
Gwamna a arewa ya bukaci FG ta bai wa jama'a damar yawo da makamai Hoto: Channels TV
Asali: UGC

A takardar, gwamnan ya ce ya zama dole gwamnati a dukkan mataki su saka hannu wurin yakar rashin tsaro da ya zama babban kalubale a kasar.

Ya sake bayyana cewa, akwai bukatar a sakarwa hukumomin tsaro kudi da kuma horar da jami'an tsaron don yakar rashin tsaron.

Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rungumi sabbin tsarin ilimi wanda zai kara wayar wa da jama'a kai.

Ya yi kira da a gyara hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta hanyar horarwa da samar musu da kayan aiki ta yadda za su kawo karshen masu shigo da kwayoyin.

Gwamna Ortom ya bada shawara a kan diban ma'aikatan tare da Samar wa matasa wurin aiki don su bar kan titi.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kama tsohon da ya sace yarinya yana bada haya don lalata da ita

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su nuna goyon baya wurin habbaka noma da kiwo ta yadda 'yan Najeriya za su samu ayyukan yi.

Gwamnan ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su saka hannu wurin yakar rashin tsaro tare da bada kariya ga rayuka da dukiyoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel