An birne tsohuwar kwamishinar da ta rasu a jihar Katsina

An birne tsohuwar kwamishinar da ta rasu a jihar Katsina

- An yi jana'izar Hajiya Amina Isah Gachi, tsohuwar kwamishinar jihar Katsina a makabartar Rimin Badawa da ke Kerau

- Ta rasu a ranar Litinin bayan gajeriyar rashin lafiya a asibitin jihar Legas inda aka yi mata aikin zuciya amma aka mayar da gawarta Katsina

- Jana'izar nata wanda Malam Mannir Isa Kerau ya jagoranta ya samu halartan daruruwan masoya da manyan jami'an gwamnati

A ranar Talata, 11 ga watan Agusta ne aka birne Hajiya Amina Isah Gachi, tsohuwar kwamishinar jihar Katsina a makabartar Rimin Badawa da ke Kerau.

Daruruwan masu ta'aziyya sun garzaya inda aka yi jana'izan wanda Malam Mannir Isa Kerau ya jagoranta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Daga cikin wadanda suka halarci wurin akwai tsohon gwamnan jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, shugaban ma'aikatan jihar, Tukur Bello Ingawa.

An birne tsohuwar kwamishinar da ta rasu a jihar Katsina
An birne tsohuwar kwamishinar da ta rasu a jihar Katsina Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sauran sun hada da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, hakimin Kurfi kuma Maradin Katsina, Ahmadu Kurfi, mijinta Hassan Kurfi da manyan sakatarorin gwamnati da ke aiki yanzu da wadanda suka yi murabus.

KU KARANTA KUMA: Ba a cika mana alkawurranmu ba - Shugabannin katolika ga FG

Maiigayiyar mai shekaru 57 ta rasu ta bar mijinta Hassan Kurfi, tsohon ma'aikacin gwamnati, 'ya'ya bakwai da jikoki.

Ta rasu a ranar Litinin bayan gajeriyar rashin lafiya a asibitin jihar Legas inda aka yi mata aikin zuciya. An mika gawar ta jihar Katsina don jana'iza da birnewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel