Buhari yana jagorantar taron FEC ta intanet karo na 11 (Hotuna)

Buhari yana jagorantar taron FEC ta intanet karo na 11 (Hotuna)

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Kasa, FEC, ta shafin intanet karo na 11 a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari sun hallarci taron a zahiri.

Buhari yana jagorantar taron FEC ta intanet karo na 11 (Hotuna)
Buhari yana jagorantar taron FEC ta intanet karo na 11 (Hotuna). Hoto daga Fadar Gwamnati
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: DSS ta kama wani da ke damfara da sunan shugaban ma'aikatan fadar Buhari

Sauran wadanda suka hallarci taron a zahiri sun hada da Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed; Ministan Kudi, Zainab Ahmed; Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire; Ministan Muhalli, Muhammad Mahmood; Ministan Shari'a, Abubakar Malami; Ministan Karafa da Ma'adinai, Olamilekan Adegbite da karamin ministan Lafiya, Olorunmibe Mamora.

Sauran ministocin kuma sun hallarci taron ne daga ofisoshinsu ta hanyar amfani da yanar gizo wata intanet.

Bayan da aka kammala rera taken Najeriya, an karrama tsaffin yan majalisar Rear Admiral Olufemi Olumide da Manjo Janar Sam Momah da suka rasu.

Olumide, wadda ya rasu a ranar 6 ga watan Agusta yana da shekaru 82 ya yi aiki a matsayin Ministan Sufuri a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon kuma ya yi ministan ayyuka lokacin mulkin Janar Murtala Mohammed.

Sam Momah ya rasu a ranar 29 ga watan Yuli yana da shekaru 77. Ya rike mukamin Ministan Kimiyya da Fasaha a zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.

A wani labarin daban, kun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata 11 ga watan Agusta ya nada Adamu Adaji a matsayin shugaban Hukumar Kula da Iyakokin Kasa, NBC.

A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya Boss Musatapha, nadin Adaji za ta fara aiki ne daga ranar Juma'a 7 a watan Agustan 2020.

Shugaban sashin watsa labarai na NBC, Ovuakporie ya ce sabon shugaban zai yi waadi ne na shekaru hudu.

Wani sashi na wasikar ta ce: "Ina farin cikin sanar da kai cewa Muhammadu Buhari, Shugaban Tarayyar Najeriya ya amince da nadin ka a matsayin Direkta Janar na Hukumar Kula da Iyakokin Kasa na tsawon shekaru hudu...

"Nadin zai fara aiki ne daga ranar 7 ga watan Agustan 2020, kuma za a fara biyan ka hakokin ka da albashi kamar yadda ya ke a karkashin doka ta albashin maaikatan gwamnati ta shekarar 2008."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel