Al-Qaeda: An bukaci DSS da 'yan sanda su zama cikin shiri a Najeriya

Al-Qaeda: An bukaci DSS da 'yan sanda su zama cikin shiri a Najeriya

- An umurci hukumomin tsaro da su zauna cikin shiri bayan rahoton da aka samu na cewa muguwar kungiyar Al-Qaeda na shigowa yankin arewa maso yammacin kasar

- Kungiyar yaki da ta'addanci ta kuma ja kunnen ‘yan Najeriya da su saka ido tare da gujewa yadda wasu kungiyoyi ke saka farfaganda a harkar tsaron arewacin kasar

- Ta ce kamata yayi a hada kai a Najeriya don tallafawa rundunar sojin kasar

An bukaci hukumomin tsaro na fararen kaya da ‘yan sanda sanda da su zauna cikin shiri bayan rahoton da aka samu na cewa muguwar kungiyar Al-Qaeda na shigowa yankin arewa maso yammacin kasar.

Gwamnatin Amurka a cikin kwanakin karshen mako ta ja kunne a kan cewa kungiyar ta’addancin na kokarin mamaye nahiyar Afrika ta hanyar amfani da annobar korona da ta samesu.

Al-Qaed: An bukaci DSS da 'yan sanda su zama cikin shiri a Najeriya
Al-Qaed: An bukaci DSS da 'yan sanda su zama cikin shiri a Najeriya Hoto: National Daily
Asali: UGC

A saboda haka ne kungiyar yaki da ta’addanci ta Najeriya ta yi kira ga ‘yan sanda, hukumar jami’an tsaro ta farin kaya da sauran cibiyoyin tsaro da su kasance a cikin shiri.

Kungiyar ta kara da jan kunnen ‘yan Najeriya da su saka ido tare da gujewa yadda wasu kungiyoyi ke saka farfaganda a harkar tsaron arewacin kasar.

A yayin jawabi a madadin kungiyar, Barista Abdulmalik Alfa ya ce kamata yayi a hada kai a Najeriya don tallafawa rundunar sojin kasar.

Kamar yadda Alfa yace, "‘yan sanda, hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi, hukumar tsaro ta farin kaya da sauran masu ruwa da tsaki dole ne su taka rawar gani wurin taimakon dakarun sojin.

“Muna son sanar da cewa akwai bukatar masu ruwa da tsaki su saka hannu wurin taimakawa dakarun sojin Najeriya don kawo karshen barazanar Boko Haram da ISWAP a kasar nan.

“Muna son kara jaddada cewa, ‘yan sanda tare da jami’an tsaro na farin kaya da su sake zuba ido a yankunan da aka shafe Boko Haram saboda dakarun sojin tashi suke ba zama ba.

“Bayan kwato yankunan da Boko Haram suka addaba, ana tsammanin sauran jami’an tsaro da su koma wurin don sake tsaresu.”

CATN ta yi kira ga dukkan kasashen da ke makwabtaka da Najeriya da su bada tallafin gaggawa don amfanin Najeriya a nahiyar Afrika.

KU KARANTA KUMA: Ba a cika mana alkawurranmu ba - Shugabannin katolika ga FG

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel