Ba a cika mana alkawurranmu ba - Shugabannin katolika ga FG

Ba a cika mana alkawurranmu ba - Shugabannin katolika ga FG

Kungiyar malaman addinin Kirista mabiya akidar katolika (CBCN), ta ce gwamnatin tarayya bata cika alkawaurran da ta dauka ba akan tsaro, yaki da rashawa da habbaka tattalin arziki a kasar nan.

A wata takarda da kungiyar ta fitar a Abuja a ranar Talata, Augustine Obiora, shugaban kungiyar, ya ce zukata na kuna a kan kashe-kashen da ake yi a yankin kudancin Kaduna.

Sun yi kira ga gwamnatocin tarayya da jihohi da su kawo karshen rashin tsaron, domin “bamu son wani dan siyasa da zai saka siyasa a kisan ‘yan Najeriya”.

Malaman addinin kiristan sun bukaci mabiya akidar katolika na dukkan kasar nan da su dauki azumin kwanaki 40 don addu’a ga ‘yan Najeriya, jaridar The Cable ta ruwaito.

Ba a cika mana alkawurranmu ba - Shugabannin katolika ga FG
Ba a cika mana alkawurranmu ba - Shugabannin katolika ga FG Hoto: The Cable
Asali: UGC

“Dole ne a tsamo masu kisan nan kuma a yanke musu hukunci. Duk inda babu adalci, ba za a samu zaman lafiya ba. A duk inda babu zaman lafiya, ba a samun ci gaba,” takardar tace.

“Duk wata gwamnati ta jiha ko ta tarayya da ke son zaman lafiya dole ne su tabbatar da adalci ga kowa. Ba za a samu ci gaba ba idan aka ci gaba da zubar da jinin jama’a saboda addini ba tare da an bi musu hakkinsu ba.

“Muna tunatar da ‘yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya ta hau mulki ne inda ta dauki alkawurran yakar rashawa, samar da tsaron rayuka da dukiyoyi da kuma habbaka tattalin arziki.

“Samar da aikin yi da tabbatar da tsayyayiyar wutar lantarki, cibiyoyin lafiya masu inganci da ilimi mai dorewa sune alkawurran gwamnatin.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya fada wa Buhari abubuwa 3 da zai yi domin shawo kan rikicin kudancin Kaduna

“Da yawa daga ‘yan Najeriya ba tare da an dubi jam’iyyun siyasa ba za a iya cewa wadannan alkawurran basu cika ba. Muna kira ga ‘yan Najeriya da su hada kansu wurin kira ga gwamnati da ta bada fifiko a kan tsare rayuka.

“Ga dukkan mabiya katolika, muna kira garesu da su yi azumin kwanaki 40 daga ranar 22 ga watan Agusta 2020 zuwa 30 ga watan Satumban 2020.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel