IPPIS: An gurfanar da tsohon ma’akacin banki da wasu Jami’ai kan zargin sata

IPPIS: An gurfanar da tsohon ma’akacin banki da wasu Jami’ai kan zargin sata

Ma’aikatan gwamnatin tarayya hudu da wani tsohon ma’aikacin banki aka kama da zargin sun saci kudi daga manhajar IPPIS na biyan albashi a Najeriya.

Jaridar The Nation ta ce ana zargin wadannan mutane ne da laifin yin wasu siddabaru a manhajar IPPIS, har su ka kai ga nasarar taba dukiyar gwamnati.

Wadanda aka su ne: Anthony Ogar, Olanrewaju Babatunde Ladipo, Joshua Ojinimi Omachonu, da Joy Write. Sai kuma wani tsohon ma’aikacin banki, Samuel Akaolisa Enwerem.

Babatunde Ladipo da Joshua Ojinimi Omachonu su na aiki ne da hukumar bincike da cigaban harkokin sama-jannati na kasa watau NSRDA.

Anthony Ogar, ma’aikaci ne a ma’aikatar gona ta tarayya da ke Abuja. Ita kuwa Joy Write, ma’aikaciyar IPPIS ce a wannan ma’aikata.

Yanzu haka Samuel Akaolisa Enwerem, ‘dan kasuwa ne da ke aikin otel a garin Abuja.

KU KARANTA: Kudin hatimi ya na samawa Gwamnati N3b a duk mako - FIRS

IPPIS: An gurfanar da tsohon ma’akacin banki da wasu Jami’ai da zargin sata
AGF Abubakar Malami
Asali: UGC

A ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, 2020, aka gurfanar da wadanda ake zargi da laifi a gaban wani babban kotun tarayya da ke Abuja.

Wani lauyan gwamnatin tarayya, Aminu Alilu, shi ne ya shigar da kara a madadin AGF. Alilu ya na tuhumar mutanen nan biyar da laifuffuka har 11.

Da aka ambatawa wadanda ake zargi jerin zargin da ke kansu, sun fadawa Alkalin kotu cewa ba su san da zaman laifuffukan ba.

A karshe Alkali mai shari’a Ahmed Mohammed, ya bada belin kowannensu a kan Naira miliyan 10, tare da sharadi da kuma karbar jinginar wanda zai tsaya masu.

Kafin nan ana cigaba da tsare su a gidan yari har sai sun cika sharadin samun beli. Lauyan gwamnati bai nuna yana da ja game da belin da Alkali ya bada ba.

Ahmed Mohammed ya ce za a koma kotu a ranar 20 ga watan Oktoba domin a cigaba da shari’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng